Dan Najeriya ya lashe gasar Al-Qur'ani a kasar Saudiya
Wani mai aikin hajji daga jihar Kaduna, Malam AbdurRahman Ahmed Salis, ya lashe gasar karatun Al-Qur’ani mai girma da massalaci mai tsarki na garin Makka, kasar Saudiya.
Da yake Magana da yan jarida a kasar Saudiya, Chiyaman na kungiyar karatun Al-Qur’ani na jihar Kaduna, De. Bello AbdulKadir, ya bayyana cewa AbdurRahman mai shekaru 24 a duniya ya sa kasar cikin alfahari da farin cikin a kasa mai tsarki.
A cewar sa, An dauki nauyin aikin hajjin AbdurRahman ne saboda ya zo na farko a lokacin gasar karatun al-Qur’ani na kasa baki daya na kamfanin Maltina, amma kuma yayi wani shiri na mussaman a massalaci mai tsarki bayan aikin hajji.
Abdulkadir ya bayyan cewa taron ya hada da karatun al-Qur’ani a cikin siga mai kyau da kuma karatun tajwidi na littafi mai tsarki.
KU KARANTA KUMA: Tanko yakasai yayi magana a kan Tinubu da Oyegun
An ba koma damar shiga shirin, ciki harda ma’aikatan masalaci mai tsarki, hukumomin tsaro da kuma mahajjata da kuma duk wanda yaga yana ra’ayin bunkasa iliminsa a kan Qur’ani:, ya ci gaba da cewa.
Chiyaman din kungiyar karatun Qur’anin ya kara da cewa a karshen taron, dan jihar Kaduna AbdurRahman Salis ya lashe kasar inda ya fito a matsayin dalibi mafi kokari an kuma basa takardun lambar yabo da dama.
A cewar sa, AbdurRahman ya taba wakiltan kasar Najeriya a gasar karatun Qur’ani na duniya a kasar Tanzania a cikin shekara ta 2013, Iran a shekara ta 2014 da kuma kasashen musulunci da dama, inda ya kawo farin ciki ga kasar.
Asali: Legit.ng