Mutumin da Aka Aika Kurkuku saboda Sata a Kasar Amurka Ya Zama Sarki a Najeriya

Mutumin da Aka Aika Kurkuku saboda Sata a Kasar Amurka Ya Zama Sarki a Najeriya

  • Ifechukwude Aninshi Okonjo II ya na cikin sarakunan da ake da su a Delta da ke yankin Kudu maso kudu
  • Kafin zamansa Sarki, ya yi rayuwa tare da Ngozi Okonjo Iweala a kasar Amurka lokacin ya na gwauro
  • An taba tura shi kurkuku saboda sata, bayan rasuwar mahaifinsu, Ifechukwude Aninshi Okonjo ya gaje shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Delta - Ifechukwude Okonjo shi ne Sarkin Ogwashi-Uku a jihar Delta, sai dai ya bar mummunan tarihi kafin darewa gadon sarauta.

A Satumban 2019 Ifechukwude Okonjo ya zama Sarkin kasar Ogwashi-Uku, a lokacin mafi yawan jama’a ba su san komai a kan shi ba.

Sarki
An taba samun Sarki Ifechukwude Aninshi Okonjo da laifi a Amurka Hoto: Getty Images/peoplesvoicenigeria.com
Asali: UGC

Labarin Ifechukwude Okonjo kafin zama Sarki

Kwanan nan jaridar Premium Times ta yi wani dogon bincike da ya nuna yadda aka taba samun Sarkin da laifi shekarun baya a Amurka.

Kara karanta wannan

"Shi ne mafi alheri" Sanata a Arewa ya fito da manufar cire tallafin mai a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya gaji sarautar ne daga hannun mahaifinsa, Farfesa Chukuka Okonjo wanda shi ne uban shugabar WTO, Ngozi Okonjo Iweala.

Shekaru bayan samun sarauta, The Cable ta taba rahoto cewa an kai masa hari lokacin da ya je yin wata ganawa da mutanen Otulu.

A shekarar 1997 wata kotu da ke Montgomery County a jihar Maryland ta samu Ifechukwude Okonjo da laifi bayan an yi shari’a.

Haka zalika an samu danuwansa Onyema Okonjo da laifi a ranar 23 ga Junairu a 1998. Shi ma yana cikin 'ya 'yan Sarkin Ogwashi-Uku.

Tuhumar Sarkin gobe da sata a Amurka

Tun Afrilun 1995 aka shigar da karar shi kotu, amma bai bayyana gaban alkali ba sai daga baya, ana tuhumarsa da sata da wani laifin.

An tuhume shi da satar kayan komfuta daga kamfanin Digital Equipment Corporation, a karshe aka ba da belinsa a kan $2,500.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya yi damfarar miliyoyin Daloli a Amurka, kotu ta daure shi

Lokacin Okonjo ya na zama tare da yaruwarsa Ngozi Okonjo Iweala ne a Amurka, bayan shekaru ta zama ministar gwamnatin Najeriya.

'Dan Sarki ya tsere zuwa Najeriya daga Amurka?

A karshe Onyema Okonjo da danuwansa duk sun samu beli amma sai suka tsere a maimakon su bayyana a kotu domin karasa shari’a.

Da aka koma kotu, sai alkali ya zartar masu da hukuncin dauri saboda kama su da laifin sata, amma babu tabbacin sun yi zaman kurkuku.

Karin zargi a kan Sarkin Ogwashi-Uku

Ko kwanakin baya Daily Trust ta ce an zargi sarkin da aikata miyagun laifuffuka iri-iri.

Masarauta ta wanke Mai martaba Ifechukwude Aninshi Okonjo II daga zargin kwacen filaye, garkuwa da mutane da sauran aika-aika.

Sarki Sanusi II, Okonjo sun samu mukami

Kwanakin baya labari ya gabata cewa Mai girma Muhammadu Sanusi II ya samu mukami a jihar Abia tare da Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.

Gwamna Alex Otti ya nada Sanusi II wanda tsohon gwamnan bankin CBN ne a wannan mukamin saboda kwarewarsa a tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng