Yanzu-yanzu: Mahaifin Ngozi Okonjo-Nweala, Farfesa Okonjo, ya rasu

Yanzu-yanzu: Mahaifin Ngozi Okonjo-Nweala, Farfesa Okonjo, ya rasu

- Mahaifin shugabar cibiyar kasuwanci ta duniya, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ya rasu

- Ya rasu a jihar Legas bayan dawowa da yayi daga kasashen Amurka da Ghana

- Basaraken farfesan ya rasu yana da shekaru 91 a duniya bayan aiki da yayi a kasashen duniya

Farfesa Chukuka Okonjo, mahaifin darakta janar ta cibiyar kasuwanci ta duniya, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ya rasu.

Daily Trust ta wallafa cewa, a wata takarda da darakta janar ta WTO, a mamadin iyalan ta fitar a ranar Litinin, tace Obi na Ogwashi-Uku da jihar Delta ya rasu yana da shekaru 91 a duniya.

"A madadin 'yan uwana na gidan sarautar Umu Obi Obahai, ina sanar da mutuwar mahaifina, Obi Farfesa Chukuka Okonjo, tsohon Obi na Ogwashi-Uku. Dan jihar Deltan ya rasu yana da shekaru 91.

KU KARANTA: Wanne 'yan bindiga zasu dauka, jan kunne ko wa'adin da ka basu?, Dawisu ga Buhari

Yanzu-yanzu: Mahaifin Ngozi Okonjo-Nweala, Farfesa Okonjo, ya rasu
Yanzu-yanzu: Mahaifin Ngozi Okonjo-Nweala, Farfesa Okonjo, ya rasu.
Asali: Original

"Ya rasu a jihar Legas bayan isowarsa daga wata tafiya da yayi zuwa Amurka da Ghana.

"Muna matukar jin dadin cewa kwanakinsa na karshe sun kasance cikin aminci kuma ya rasu kamar yadda yayi rayuwarsa cike da aminci," yace a wata takarda.

Dr Okonjo-Iweala tace mahaifinta ya kasance masani da ake mutuntawa, ma'aikacin da yayi aiki a kasashe da dama kuma basaraken gargajiya ne.

Marigayi Obi yana da digiri a fannin lissafi daga wata jami'a a Londo, digirin digir a fannin lissafi daga Erlangen, Jamus, digirin digir a fannin tattali daga Erlangen, Jamus da digirin digir daga Cologne, Jamus.

KU KARANTA: NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode a ranar Litinin, 15 ga watan Maris ya kushe kisan gillar da aka yi wa Fulani 6 'yan gida daya a jihar Osun.

Fani Kayode wanda ya nuna damuwarsa a kan aukuwar mummunan lamarin, ya ce an haresu ne ganin basu da yadda zasu kare kansu.

Ya sanar da hakan ne a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter inda yace kisan gillar bai dace ba kuma babu jarumta a ciki.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel