Osinbajo Ya Gaji da Halin da Tinubu Ya Jefa Al'umma, Ya Tsoma Baki, Ya Nemo Mafita
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya nuna damuwa kan yadda tsadar rayuwa ta dabaibaye Najeriya gaba daya
- Farfesa Osinbajo ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta samar da hanyoyin inganta rayuwar al'umma duba da halin da ake ciki
- Osinbajo ya shawarci Bola Tinubu ya mayar da hankali wurin samar da lafiya da rage radadin da al'umma ke ciki a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yi magana kan halin kunci da yan Najeriya ke ciki.
Yemi Osinbajo ya bukaci Bola Tinubu da ya mayar da hankali wurin inganta rayuwar al'ummar Najeriya duba da halin da ake ciki.
Yemi Osinbajo ya shawarci Tinubu kan halin kunci
Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne yayin wani babban taro kan rawar da mata ke takawa a harkokin kasuwanci, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Osinbajo ya bukaci inganta rayuwar al'umma da ba su ingantaccen lafiya saboda wahalar da ake sha.
Ya ce yadda kayayyakin masarufi suka yi tsada a Najeriya ya fara kashe musu guiwa kan rayuwa a ƙasar.
"Tsadar rayuwa ta fara wuce gona da iri da har yan Najeriya sun fara cire rai game da kasar."
"Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ba da karfi wurin inganta rayuwar al'umma musamman ta bangaren abinci."
- Yemi Osinbajo
Farfesa Osinbajo ya damu da halin da ake ciki
Osinbajo ya koka kan yadda yan kasar ke fama da tsadar rayuwa musamman kayan masarufi da ke neman fin ƙarfin al'umma.
Ya ce ya kamata gwamnati ta samar da tsaro musamman a bangaren abinci saboda muhimmancinsa a rayuwar al'umma.
Osinbajo ya fadi wanda yafi sanin Buhari
A baya, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana litaffin Femi Adesina a matsayin 'mai cike da hikima kuma kan lokaci'
Yemi Osinbajo ya ce littafin ya bada 'mafi ingancin' yadda abubuwa ke faruwa a fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock a Abuja.
Farfesa Osinbajo ya yi wannan jawabin ne a Legas lokacin da Adesina ya gabatar masa da kwafin littafin a hukumance.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng