Jerin Kasashen Afrika 5 da Suka Fi Bata Lokaci a Kafofin Sadarwa Ta Zamani

Jerin Kasashen Afrika 5 da Suka Fi Bata Lokaci a Kafofin Sadarwa Ta Zamani

A zamanin nan, kafofin sadarwa suna taka muhimmiyar rawa wurin inganta harkokin kasuwanci da gwamnatoci da sauran fannonin rayuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

A kasashen Afirka da dama kafofin sadarwa sun koma hada al'umma wuri guda da yada labarai wanda ya yi matukar tasiri a cigaban Nahiyar.

Kasashen Afrika da suke fi amfani da kafofin sadarwa
Najeriya da sauran kasashen Afrika 4 da suka fi amfani da kafofin sadarwa. Hoto: Xavier Lorenzo.
Asali: UGC

Business Insider Afrika ta fitar da wani rahoto yadda wasu mutane a kasashen Afirka ke bata lokutansu a kafofin sadarwa a kullum.

Mafi yawan wadanda suka fi bata lokaci a kafofin sadarwa matasa ne maza da mata wadanda ake ganin hakan zai shafi rayuwarsu nan gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Majalisa ta fitar da sabon kuduri da zai yi wa kujerar shugaban kasa barazana

Legit Hausa ya duba muku ƙasashen Afrika biyar da suka fi bata lokaci a yanar gizo.

1. Kenya - Awanni 3 da mintuna 43

Kasar Kenya ta kasance ta farko a jerin kasashen Nahiyar Afirka da suka fi bata lokaci a kafofin sadarwa.

Akalla yan kasar na shafe fiye da awanni uku a kullum kan yanar gizo da ke da matukar tasiri a yanzu.

A Kenya, mutane sun dauki kafofin sadarwa a matsayin hanyar sadarwa da bangaren kimiyya da harkokin kasuwanci.

2. Afirka ta Kudu - Awanni 3 da mintuna 37

Kasar Afrika ta Kudu ta zamo na hudu a Nahiyar wurin yawan amfani da yanar gizo a kullum, The Nation ta ruwaito.

Yan kasar da ke Kudancin Afrika na shafe akalla awanni uku da mintuna 37 a yanar gizo wanda wasu ke ganin hakan zai sauya akalar Afrika ta Kudu.

Manhajojin Facebook da Whatsapp sune suka fi tasiri a kasar wurin yada labarai da inganta fannonin fasaha.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Magoya bayan APC sun fantsama majalisa kan tsadar rayuwa

3. Najeriya - Awanni 3 da mintuna 23

Kasar Najeriya da ke Afirka ta Yamma ta kasance ta uku a jerin kasashe da kafofin sadarwa ke da tasiri matuƙa.

Matasan kasar na yawan amfani da kafofin sadarwa wurin muhawara ta siyasa da kasuwanci da kuma yada al'adu da wasu bayanai.

Yan kasar na shafe akalla awanni uku da mintuna 23 a kullum wanda ke ba kamfanoni da dama riba a duk wayewar gari.

4. Ghana - Awanni 2 da mintuna 43

Al'ummar kasar Ghana sun yi kaurin suna wurin amfani da kafofin sadarwa inda suke shafe fiye da awanni biyu a kullum, cewar BusinessDay.

Mafi yawan masu amfani da yanar gizo a Ghana sun mayar da hankali wurin gwagwarmayar neman yanci da ilimi da kuma ɓangaren nishadi.

Manhajojin Facebook da Whatsapp da kuma TikTok sun fi tasiri a kasar musamman a bangaren matasa.

5. Masar - Awanni 2 da mintuna 41

Kara karanta wannan

Sweden: Kotu ta daure dan gwagwarmaya a gidan kaso kan kona Alkur'ani, ya yi martani

Kasar Masar tun ba yau ba ta yi suna wurin amfani da kafofin sadarwa a yankin Arewacin Afirka da ma Nahiyar baki daya.

Kafofin sadarwa sun kasance hanyar yada labarai da bangaren nishadi da hada kan al'umma duk da dokoki da suka dabaibaye ɓangaren.

Mafi yawan kafofin sadarwa da aka fi amfani da su a Masar ba su wuce manhajojin Facebook da kuma Whatsapp ba.

Hanyoyin sadarwa a kasar Hausa

Kun ji cewa a kasar Hausa a zamunna da suka shude, ana amfani ne da kafafen sadarwa ne wajen yada bayanai, sanarwa da isar da sakon hukuma ko masarauta ga talakawansu.

A wadancan lokuta, babu lantarki, babu yanar gizo, babu jirage, ba kuma kowa ne ya iya rubutu ba, balle karatu, don haka, magana ta fatar baki ita take isar da sakonni.

A wasu lokuta akan kada kayan kida ko amsa kuwwa, domin a jawo hankalin mutane ga sakon da ake son bayarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.