'Ka da Ku Dogara da Gwamnati': Sanata Ya ba Matasan Najeriya Sirrin Neman Kudi

'Ka da Ku Dogara da Gwamnati': Sanata Ya ba Matasan Najeriya Sirrin Neman Kudi

  • Dan majalisar dattawa, Adeniyi Adegbonmire ya nemi matasa da su rage dogaro da neman aikin gwamnati bayan kammala karatu
  • Sanatan mai wakiltar mazabar Ondo ta tsakiya ya bayyana hakan ne a wajen wani taron ba matasa horo da ya shiryawa matasa
  • Sanata Adegbonmire ya yi nuni da cewa a yanzu gwamnati ba ta ba da aiki don haka akwai bukatar matasa su koyi sana'o'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Sanata mai wakiltar Ondo ta tsakiya a jihar Ondo, Adeniyi Adegbonmire (SAN), ya yi kira ga matasan Najeriya da su rungumi sana'o'in dogaro da kai.

Sanata Adegbonmire Adeniyi ya ce ya kamata matasa, musamman wadanda suka kammala digiri su kama sana'o'i tare da rage dogaro ga neman aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

Pantami da mutane sun fusata da maka kananan yara a Kotu saboda zanga zanga

Sanatan Ondo ya aika sako ga matasan Najeriya kan batun neman aikin gwamnati
Sanatan Ondo ya bukaci matasan Najeriya su kama sana'o'i tare da rage dogaro da gwamnati. Hoto: Adeniyi Adegbonmire SAN
Asali: Facebook

'Aikin gwamnati ba tabbas' - Sanata Adeniyi'

Sanatan ya bayyana cewa yanzu aikin gwamnati ba shi da wani tabbas kuma ita kanta gwamnatin ba za ta iya ba kowa aiki a kasar ba, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda hakan, dan majalisar dattawan ya ce akwai bukatar duk wanda ya kammala karatunsa ya yi tunanin koyon sana’o’in da zai dogara da kansa.

Sanata Adeniyi ya bayyana hakan ne a garin Akure, babban birnin Ondo a wani taron ba da horon sana'o'i ga wadanda suka kammala jami'a daga mazabarsa ta Ondo ta tsakiya.

Sanata ya horar da matasan mazabarsa

Shirin ba da horon wanda aka fara daga ranar Litinin zai ba matasa sama da 170 horo har zuwa ranar Laraba, kuma sanatan ne ya dauki nauyi.

An ce shirin na kwanaki uku wanda sanatan ya dauki nauyi ya kuma samu hadin gwiwar hukumar fadada ayyukan noma da bincike ta kasa.

Kara karanta wannan

Zanga Zanga: Lauyan gwamnatin Tinubu ya fayyace dalilin maka ‘kananan’ yara a kotu

Dan majalisar na tarayya ya bayyana cewa ya ba matasan mazabarsa wannan horo ne domin ya dauke su aiki a fannin da suka samu horon.

'Ku koyi sana'a, babu aikin gwamnati' - Sanata

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Ajibola Basiru, ya shawarci 'yan bautar kasa da su nemi sana'o'in dogaro da kai maimakon jiran samun aikin gwamnati.

Sanatan ya shawarci matasan Najeriya da su tabbatar sun habaka kwarewar kasuwancinsu domin dacewa da yanayin tattalin arziki na yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.