VAT: 'Yan Najeriya na Fama da Kansu, Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Kara Haraji

VAT: 'Yan Najeriya na Fama da Kansu, Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Kara Haraji

  • Bayan ta sha musanta cewa za ta kara VAT, gwamnatin Najeriya ta ce shirin gwamnati na kara harajin ya yi nisa
  • Ministan kudi da tattalin arziki na kasa ne ya bayyana haka a taron masu zuba hannun jari da ya gudana a Washignton DC
  • Mista Wale Edun ya ce majalisar tarayya na duba batun karin harajin, kuma ana sa ran kayan alatu za a yi wa sabon karin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaGwamnatin tarayya ta tabbatar da shirinta na kara harajin VAT da yan kasar nan su ke biya kan kayayykin da su ke saye.

Kara karanta wannan

"Ba Dole ba ne:" Najeriya ta soma nuna yiwuwar botsarewa shawarwarin IMF

Ministan Kudi da tattalin arziki, Wale Edun ne ya tabbatar da shirin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi ga taron masu zuba hannun jari a taron IMF da Bankin Duniya a Washignton DC.

Tinubu
Najeriya za ta kara harajin VAT da 15% Hoto: PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ministan na cewa har yanzu gwamnatin Najeriya na duba lamarin gabanin ayyana karin da za a yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanne kaya za a karawa harajin VAT?

Jaridar Solacebase ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce ana shirin kara harajin VAT da 15% a kan kayan alatu da jama’a ke saye.

Gwamnatin ta bayyana cewa yanzu haka batun karin harajin na gaban majalisar tarayya ta na nazari a kai, gabanin tabbatar da karin.

Yadda za a kara harajin VAT a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce kayayyakin amfanin yau da gobe da talakawa ke amfani da su ba sa daga cikin wadanda za a karawa harajin VAT.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Gwamnati ta fadi yadda za a hana Dala tashi kan Naira

Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa za a sanar da jama’a kayayyakin da ba za a karawa harajin ba a nan gaba kadan.

Gwamnati za ta kara harajin VAT

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce ana duba yiwuwar kara harajin VAT da ta ke karba idan yan kasar nan sun sayi kaya ko wanda aka sayar daga 7.5% zuwa akalla 10%.

Kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sauye-sauyen haraji da ya gabatar da kudurin, y ana kuma fatan za a kara kudin VAT da ake ba wa jihohi da kananan hukuma zuwa 90%.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.