EFCC Ta Dura Gidan Rediyo Ana tsaka da Watsa Shiri Kai Tsaye, NBC Ta Dauki Zafi
- Hukumar NBC ta yi Allah wadai da samamen da jami'an hukumar EFCC suka kai gidan rediyon Urban FM 94.5 da ke Enugu
- A cewar wani rahoto, jami’an EFCC sun mamaye gidan rediyon ne da nufin cafke mai gabatar da wani shiri “Prime Time”
- A sanarwar da ta fitar, NBC ta yi Allah wadai da salon aikin EFCC tana mai duba da yadda shirin ke da tasiri ga masu sauraro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar 14 ga watan Oktoba ne aka rahoto cewa jami'an hukumar EFCC sun kai samame gidan rediyon Urban FM 94.5 da ke Enugu.
An ce jami'an EFCC sun mamaye gidan rediyon a yayin da ake watsa shirin "Prime Time" na kai tsaye, da nufin cafke mai gabatarwa, Favor Ekoh.
NBS ta yi Allah wadai da samamen EFCC
Hukumar kula da kafafen watsa labarai na Najeriya, NBC ta fito ta yi Allah wadai da samamen da jami'an EFCC suka kai gidan rediyon Urban inji rahoton This Day.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktar Hulda da jama’a ta NBC, Susan Obi, ta bayyana rashin jin dadin hukumar game da lamarin, ta jaddada kudirin NBC na kare martabar cibiyoyin labaran Najeriya.
NBC tana kallon kutsen a matsayin cin zarafin dokokin watsa labarai, musamman tun da ya faru a lokacin da ake gabatar da shirin kai tsaye.
Kutsen EFCC: Hukumar NBC ta ba da hakuri
A cewar rahoton Premium Times, NBC ta soki salon aikin na EFCC, ta bayyana cewa bai dace ba, kuma zai iya haifar da rudani, hargitsi da fargabar jama’a.
Tribune ta rahoto hukumar NBC ta bayar da hakuri ga masu sauraren gidan rediyon, jama'ar jihar Enugu da masana'antar yada labarai kan abin da EFCC ta yi.
Sun bukaci jama’a da su kasance masu bin doka da oda yayin da ake gudanar da shari’a tare da tunatar da kafafen yada labarai da su kiyaye ka’idojin da’ar aikinsu.
Gwamnati ta garkame gidan rediyo
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Ribas ta garkame gidan talabijin na Africa Independent Television da gidan rediyon Raypower FM.
An ce injiniyoyin sadarwa da gwamnatin jihar ta dauka ne suka katse ayyukan kafofin watsa labaran tare da rufe gidajen a lokacin da suka je da jami’an tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng