Matsalar Tsaro: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Rediyo Najeriya
- Wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari gidan Rediyo Najeriya dake Ibadan, jihar Oyo
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun yi kokarin ɗaukar fansa ne a akan jami'an tsaron sa kai dake da ofishi a ciki
- Sai dai isar su ke da wuya suka tarad da ba ko ɗaya daga cikin waɗanda suka kawo wa harin
Ibadan:- Wasu yan bindiga sun kai hari kafar watsa labarai ta rediyo Najeriya dake Moniya, Ibadan, jihar Oyo, kamar yadda punch ta ruwaito.
Yayin harin yan ta'addan sun yi kaca-kaca da motoci, gilasan jikin kofa, da na tagogin dake kafar watsa labaran.
Rahotanni sun bayyana ne cewa maharan sun kai wannan harin ne domin ɗaukar fansa biyo bayan wani farmaki da jami'an tsaro suka kai maɓoyar yan ta'addan a yankin Sasa ranar Asabar.
2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe
Yan bindigan sun shiga gidan rediyon ne domin ɗaukar fansa kan yan bijilanti, mafarauta waɗanda suka fara kai musu hari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meya kawo harin ɗaukar fansa?
Yayin harin da jami'an tsaron sa kai na bijilanti da mafarauta suka kaiwa yan bindiga, sun kashe musu mutum ɗaya.
Mutuwar wannan ɗan ta'addan ne yasa yan uwansa suka yi fushi suka kai hari FRCN inda suke tsammanin mafarautan Soludero ke da ofishi.
Kakakin yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso ya tabbatar da kai harin a wani jawabi ranar Lahadi.
Wani ɓamgaren jawabin yace:
"Bayan wata fafatawa da ta gudana tsakanin jami'an tsaron bijilanti, mafarautan Soludero da wasu tawagar yan bindiga ranar Asabar a yankin Sasa, inda wani daga cikin yan ta'addan yaji muggan raunuka daga baya aka tabbatar ya mutu."
"Bayan haka ne yan bindigan da yawan su suka kai hari ofishin Soluderu dake harabar gidan Rediya Najeriya Amuludun 99.1 FM, Moniya Ibadan domin ɗaukar fansa."
"Binciken da muka yi ya nuna cewa yayin da yan ta'addan suka isa harabar gidan rediyon sai suka harzuka saboda babu ko ɗaya daga cikin abun harinsu. Hakan yasa suka farfasa gilasan motoci huɗu da na kofofi."
PPRO ɗin ya ƙara da cewa zasu kamo waɗanda suka yi hakan domin gurfanar da su a gaban kotu.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama
Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa harin, wanda ya bar mutane da dama cikin raunuka, ya faru ne lokacin mutane na bacci ranar Asabar da daddare.
Asali: Legit.ng