Cin Hancin $500,000: Tsohon Dan Majalisar Kano Ya Shaki Iskar Yanci, Ya Bar Gidan Yari
- Tsohon dan Majalisar Tarayya a jihar Kano, Farouk Lawan ya samu yanci bayan kama shi da cin hanci da rashawa
- An zargin tsohon dan Majalisar da karbar cin hanci na makudan kudi har $3m a hannun dan kasuwa, Femi Otedola
- Wannan na zuwa ne bayan daure tsohon dan Majalisar har na tsawon shekaru biyar a gidan gyaran hali a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano, Hon. Farouk Lawan ya shaki iskar yanci.
An zargi Hon. Farouk Lawan da nema da kuma karbar cin hanci na makudan kudi har $500,000.
Kano: Zargin da ake yi wa Farouk Lawan
Punch ta ruwaito cewa Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin da aka yanke kan zargin Farouk a ranar 26 ga watan Janairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An same shi da laifin karbar $3m daga fitaccen dan kasuwa a bangaren man fetur, Femi Otedola.
Lamarin ya faru ne lokacin da Farouk Lawan ke riƙe da shugaban kwamitin binciken badakalar tallafin mai a 2012.
Daily Nigerian ta wallafa wani faifan bidiyon Hon. Farouk Lawan bayan sakinsa a yau Talata 22 ga watan Oktoban 2024 a shafinta na X.
Karanta wasu labarai game da Farouk Lawan
- Abu 6 da ya kamata ka sani kan Farouk Lawan, mutumin da aka jefa Kurkuku
- Tsohon Bidiyo ya nuna lokacin da Farouk Lawan ya rika sunkuma cin hancin Daloli a 2012
- An yanke wa tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan ɗaurin shekaru 7 kan cin hanci na $500,000
Kotu ta ragewa Farouk zaman gidan kaso
A baya, kun ji cewa Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke wa tsohon dan majalisa, Farouk Lawan, hukuncin bayan gamsuwa da cewa ya amshi rashawar $500,000 a 2012.
An yanke wannan hukuncin ne a ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairun 2022 bayan kotun ta wanke dan majalisar laifuka biyu da aka daure shi akan su.
Da kyar kotun ta amince da wannan hukuncin sannan ta rage masa lokacin da zai yi a gidan gyaran halin, daga shekaru bakwai zuwa shekaru biyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng