Tsohon Bidiyo ya nuna lokacin da Farouk Lawan ya rika sunkuma cin hancin Daloli a 2012

Tsohon Bidiyo ya nuna lokacin da Farouk Lawan ya rika sunkuma cin hancin Daloli a 2012

  • A shekarar 2012 Farouk Lawan ya karbi cin hanci a hannun Femi Otedola
  • Hon. Lawan yana bincike ne a kan kamfanonin da suka ci kudin tallafin mai
  • Daga baya Attajirin ya fallasa abin da ya faru tsakanin sa da ‘Dan Majalisar

A farkon makon nan ne aka yanke wa tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Farouk Lawan, hukuncin dauri, bayan shekara bakwai ana shari’a a kotu.

An samu Hon. Farouk Lawan da laifin neman cin hancin $3m, da karbar $500, 000 a cikin kudin, domin a rufa wa kamfanin man Mista Femi Otedola asiri.

ICPC ta ce tsohon ‘dan majalisar ya karbi kudi a hannun kamfanin Zenon Oil and Gas Ltd da nufin goge sunansu a cikin wadanda suka ci kudin tallafin fetur.

KU KARANTA: Abin da ya kamata ka sani a kan Farouk Lawan

Jaridar The Cable ta yi waiwaye adon tafiya, ta dauko lokacin da wannan ‘dan siyasa ya karbi sahun farko na wannan kudi, an yi wannan ne a gidansa.

Femi Otedola ya shirya wa Farouk Lawan gadar zare

Abin da Hon. Lawan bai sani ba shi ne attajirin ya tuntubi hukumar DSS masu fararen kaya kafin ya bada wannan kudi, aka shirya yadda za a cafke shi.

Bayan karbar dalolin kudi, sai Lawan ya kawo kudiri a gaban majalisa, ya na neman a cire sunan Zenon Oil and Gas Ltd daga kamfanonin da ba su da gaskiya.

Wannan lamari ya bata wa ‘dan siyasar suna a Najeriya, bayan kowa ya na yi masa kallon mai gaskiya, sai aka ji ai an ba shi daloli domin a toshe masa baki.

Farouk Lawan a kotu
Hon. Farouk Lawan Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Karshen cin amana: Maigida ya yi ram da Amininsa ya je kwartanci a gidansa

Shi dai Otedola ya yi amfani da wannan, ya tona abin da ya faru tsakaninsa da Lawan a duhun dare, ya ce ya yi abin da ake nema ne saboda a kama maras gaskiya.

Jaridar ta kawo bidiyon abin ya wakana, inda aka dauki hoto ba tare da Lawan ya ankara ba. Za a gan shi ya na karbar wasu daga cikin Dala miliyan 3 da ya bukata.

Yanzu maganar da ake yi, Farouk Lawan mai shekara 56 yana daure a gidan yarin Kuje, Abuja.

A ranar Talatar nan aka ji cewa wata Kotu a Abuja ta yanke wa tsohon dan majalisar na yankin Bagwai da Shanono a jihar Kano hukuncin dauri a gidan gyaran hali.

Farouk Lawan ya nemi Femi Otedola ya bada cin hanci domin a cire kamfaninsa cikin wadanda za a bincika game da badakalar tallafin man fetur a wancan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel