Yanzu-Yanzu: An yanke wa tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan ɗaurin shekaru 7 kan cin hanci na $500,000

Yanzu-Yanzu: An yanke wa tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan ɗaurin shekaru 7 kan cin hanci na $500,000

  • Kotu a Abuja ta yanke wa tsohon dan majalisa Farouk Lawan hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan gyaran hali
  • Hakan ya biyo bayan samunsa da laifin karbar cin hanci na $500,000 ne daga hannun Femi Otedola
  • Farouk Lawan ya nemi Femi Otedola ya bada cin hancin ne domin a cire kamfaninsa cikin wadanda za a bincika game da badakalar tallafin man fetur

Wata babban kotun da ke birnin tarayya Abuja ta yanke wa Hon. Farouk Lawan, tsohon dan majalisar wakilai na Nigeria daurin shekaru bakwai a gidan gyaran hali saboda samunsa da laifi a cin hanci a badakallar tallafin kudin man fetur, Daily Trust ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa an samu Lawan ne da laifin nema da karbar cin hanci daga hannun biliniyan dan kasuwa Femi Otedola yayin binciken badakalar tallafin kudin man fetur a 2021.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa Farouk Lawan ɗaurin shekaru 7 saboda cin hanci
Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa Farouk Lawan ɗaurin shekaru 7 saboda cin hanci
Asali: Original

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Buhari ya umurci Pantami, Fashola da wasu ministoci su tattauna da Twitter

Lawan ne ya jagoranci kwamitin wucin gadi da aka kafa don bincike kan zargin rashawa a batun badakalar na kudin tallafin man fetur a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Otedola ya yi zargin cewa Lawan ya nemi kamfaninsa na Zenon Petroleum and Gas Limited ta bada cin hanci na Dalla miliyan 3 domin a cire ta cikin jerin kamfanonin da za a bincika.

Hukumar yaki da cin rashawa na ICPC ta yi karar Lawan kan zarginsa da karbar rashawar $500,000 daga hannun Otedola.

KU KARANTA: Bangarori biyu na jam'iyyar APC sun yi rikici, an harbi mutum biyu wasu da dama sun jikkata

Hukuncin da kotu ta yanke

An same shi da laifi a kan tuhuma na farko, biyu da uku game da karbar cin hanci daga hannun Otedola.

An yanke masa hukuncin shekaru bakwai kan tuhumar farko yayin da aka yanke masa shekaru biyar a kan tuhuma a uku.

Za a gwamutse masa hukuncin zaman gidan yarin ne.

An kuma umurci Lawan ya mayarwa gwamnatin tarayya $500,000 da ya karba daga hannun Femi Otedola.

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Cross Rivers ta bada kwangilar a siyo mata tsintsiya guda miliyan uku daga masu siyarwa a kasuwanni don sabbin mutanen da suka shiga jam'iyyar, Premium Times ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Bassey Ita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Calabar.

Mr Ita ya ce an gano kwastam an samu karancin tsintsiya a jihar, wanda shine alama na jam'iyyar, bayan mutane da yawa sunyi tururuwan shiga jam'iyyar bayan gwamnan jihar Ben Ayade ya shigo jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel