Babban Limamin Imo Ya Bayyana Kalubalen da Musulmi Ke Fuskanta a Kudu maso Gabas

Babban Limamin Imo Ya Bayyana Kalubalen da Musulmi Ke Fuskanta a Kudu maso Gabas

  • Babban limamin Imo, Sheikh Suleiman Njoku, ya bayyana kalubalen da musulmi 'yan kabilar Ibo ke fuskanta a Kudu maso Gabas
  • Malamin ya lura da yadda ta'addanci da ayyukan 'yan fashi a Arewa ke shafar fahimtar addinin musulunci a tsakanin al'ummar Ibo
  • Duk da wannan kalubale, Sheikh Njoku ya lura cewa addinin Musulunci na bunkasa a Imo inda ya zuba jari a ilimin addini a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo – Sheikh Suleiman Njoku, babban limamin jihar Imo ya bayyana irin kalubalen da musulmi ‘yan kabilar Ibo ke fuskanta a yankin kudu maso Gabas.

Galibi dai kabilar Ibo ne suka mamaye Yankin Kudu maso Gabas inda da yawansu ke kan tafarkin addinin Kirista baya ga addinin gargajiya.

Kara karanta wannan

An bude kasuwar Musulunci ta farko a Najeriya, inda kayan abinci suke da araha

Sheikh Suleiman Njoku ya yi magana kan halin da Musulmi ke ciki a Kudancin Najeriya
Babban limamin Imo, Sheikh Njoku, ya bayyana kalubalen da ‘yan kabilar Igbo ke fuskanta a Kudu. Hoto: @haruna_braimoh
Asali: Twitter

A wata hira da jaridar The Punch ta wallafa, Sheikh Njoku ya ce Musulmai na fuskantar wasu manyan kalubale a yankin Kudu maso Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban kalubalen da Musulmi ke fuskanta a Kudu shi ne cakudewar al'adu da addini, wanda hakan ke iya haifar da kaucewa koyarwar Musulunci inji malamin.

Rikicin Arewa ya shafi Musulman Kudu

Sheikh Njoku ya yi nuni da cewa ayyukan Boko Haram da ‘yan bindiga a yankin Arewacin kasar, ya shafi yadda ‘yan kabilar Ibo ke mu’amala da ‘yan uwansu da suka musulunta.

Ya bayyana cewa, ana samun sabani tsakanin al’ummar Ibo kan cewa wasu halaye da 'yan Arewa ke nunawa sun yi daidai ne da koyarwar addinin Musulunci.

Sheikh Njoku wanda kuma shi ne shugaban kungiyar limaman Imo ya ce irin wannan rashin fahimtar tasa ake gargadar wadanda suka shiga Musulunci a jihar.

Kara karanta wannan

An nada dan kabilar Ibo na farko a matsayin babban limanin masallacin Abuja

Ya ce ana gargadar su da su kauracewa duk wani abu da ya shafi ta'addanci ko kuma yunkurin shigo da ayyukan 'yan Boko Haram a cikin garuruwan Imo.

"Ibo ba sa son auren musulmi" - Sheikh Njoku

Da aka tambaye shi ko Musulmin yankin Ibo na fuskantar wariya, Sheikh Njo ya ce:

"Idan kai Musulmi ne kana shan wahala kafin ka samu aikin gwamanti a jihar, amma Ibo suna zuwa garuruwan Musulmi ana basu aiki ba tare da tsangwaman ba.
"A jihar Imo, da zarar sun ga kana da amfani da sunan Musulmi, za su cire ka daga cikin wadanda za a dauka aiki, za su ce ka je Arewa ka nemi aiki a can.
“Har ila yau, matan mu ba za su iya sanya hijabi saboda tsoron kai hari, idan sun sanya hijabi za a ce da su 'yan Boko-Haram ne.
"Ibo ba sa son auren musulmi, kuma suna adawa da masu sha'awar auren musulman. Mu dai kullum muna tausasar zuciyar al'umma, bin tafarkin Allah shi ne sauki a garemu."

Kara karanta wannan

"Kuna da damar taimakon ƴan Najeriya," Jigon APC ya dura kan Kwankwaso da Atiku

'Abin da ya sa aka tsani Musulunci' - Armstrong

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar marubuciya mai suna Karen Armstrong ta ce mutane sun tsani addinin ne saboda suna tunanin yana da rinjaye a duniya,

Karen Armstrong wadda ta taba kasance babbar jigo a addinin Kirista ta yi nuni da cewa mutane masu fahimta ne kadai suka fahimci addinin Musulunci da kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.