Harin Musulmin Ƙabilar Igbo: MURIC ta buƙaci a gurfanar da Rev Fr. Onah
- Kungiyar MURIC ta ce tana tare da NSCIA kan karar da ta shigarwa DSS kan kama Rev. Onah
- Shugabannin addinan da ke amfani da mumbari don haddasa fitina basu da kima
- Muna saka ido muga matakin da Hukumar 'Yan sandan farar Hula, DSS, za ta dauka a kan
Ƙungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta bukaci a kama kuma a gurfanar da Rev. Fr. Godfrey Igwebuike Onah, wata huduba da ya yi a coci na tunzura matasan kiristoci a Nsukka, jihar Enugu, da su kai hari kan musulmai da kuma lalata masallatai a garin.
Shugaban MURIC, Ishaq Akintola, wanda ya yi wannan batun a ranar Juma'a a wata sanarwa, ya ce kungiyar ta goyi bayan Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) a karar da ta shigarwa DSS na a kama tare da gurfanar da Rev. Onah.
DUBA WANNAN: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa
"MURIC na da wani faifen bidiyo wanda Rev. Fr. Godfrey Igwebuike Onah ya ke tunzura kiristoci kwanaki da suka gabata.
"Limamin kiristan ya bayyana cewa, 'Bazai yi wu anan garin Nsukka wasu musulmi su dame da kiran sallah tun 4:00 na Asubah ba...'
"Ko shakka babu wannan umarni ne na a yaki musulmi a kuma lalata masallatai a Nsukka, kai in ta kama ma, gaba daya yankin kudu maso gabas.
"An kona masallatai biyu yadda baza a iya gane su ba cikin sati guda da kalaman tunzurawar.
"An kuma kai hari kan Musulmi har an ji wa wasu raunika," a cewar Akintola.
A abin da yake gani, hudubar Rev. Onah tana cike da kalamai masu ɗaci da nuna kiyayya; kuma dole sai an dauki mataki akan irin wadannan ko kuma rashin lafiya ya addabi kowa.
"Shugabannin addinai, wanda suke haddasa fitina su kuma zuba ido yayin da kalaman ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi sun rasa kimar da za a girmama su a matsayin shugabanni.
KU KARANTA: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona
"Idan za a iya tunawa NSCIA ta shigar da kara a wajen shugaban DSS.
"Muna bibiyar lamarin kuma zamu gani in DSS za suyi abin daya dace ko a'a.
"Yana da kyau DSS su dauki mataki saboda dalilai uku.
"Na ɗaya, zai sa wanda abin ya shafa su ji akwai yiwuwar a bi musu hakkin su; na biyu, zai zama Izina ga sauran shugabannin addinai wanda ke son yin amfani da mumbari don kunna wutar rikici; Musulman da ransu ya ɓaci saboda harin da aka kaiwa yan Uwansu zasu rusuna," a cewar kungiyar.
A wani labarin daban, shaharren mutumin nan ma kama barayi da 'yan fashi a Najeriya Ali Kwara Azare ya rasu a ranar Juma'a 6 ga watan Nuwamban 2020.
Ali Kwara ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da jinya kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng