Musulunci addini ne mai matukar rinjaye shine yasa mutanen duniya suka tsane shi - Karen Armstrong

Musulunci addini ne mai matukar rinjaye shine yasa mutanen duniya suka tsane shi - Karen Armstrong

- Musulunci addini ne mai cike da dabaru wanda mutane masu fahimta ne kadai suka fahimci addinin da kyau

- A lokacin da aka tambayeta a kan ta’addanci a Musulunci, marubuciyar ta ce Qur’ani ba magana kadai yayi a kan jihadi ba

- Tsohuwar ma’abociya akidar katolika ta addinin Kiristar ta sadaukar da rubuce-rubucenta ne a kan bincike da kamanceceniyar addini

Musulunci addini ne mai cike da dabaru. Mutane masu fahimta ne kadai suka fahimci addinin da kyau. A wata tattaunawa da aka yi da wata marubuciya mace wacce ta karba lambobin yabo, ta bayyana cewa addinin ne mai matukar rinjaye.

Matar wacce marubuciya ce ta kare Musulmai da Qur’an. Ta ce mutane sun tsani addinin ne saboda suna tunanin yana da rinjaye. Babbar marubuciyar mai suna Karen Armstrong ta sanar da hakan ne yayin da aka tattauna da ita a kan Musulunci.

Musulunci addini ne mai matukar rinjaye shine yasa mutanen duniya suka tsane shi - Karen Armstrong
Musulunci addini ne mai matukar rinjaye shine yasa mutanen duniya suka tsane shi - Karen Armstrong
Asali: Facebook

A lokacin da aka tambayeta a kan ta’addanci a Musulunci, marubuciyar ta ce Qur’ani ba magana kadai yai a kan jihadi ba.

Tattauanwar ta bayyana ne a El Mundo a kan yadda marubuciyar ta Musulunci ke fuskantar kalubale mai tarin yawa saboda karfin rinjayen shi a duniya.

Kamar yadda Armstrong ta bayyana, Qur’ani ya kunshi gina jama’a ne masu madaidaiciyar dama amma sai ake amfani da shi wajen kare ta’addanci.

KU KARANTA: Bidiyo: An kama wasu yara da suka boye a cikin wani katafaren shago suka ci abinda suke so suka more

Ta ce ayoyin jihadi duk ba a fara amfani da su ba sai bayan shekaru 400 bayan da wayewar addinin Musuluncin.

"Bayan shekaru 400 da mutuwar Annabi Muhammad, lokacin da gabas da yamma suka hare su, shugabannin sai suka ba wa jama’a karfin guwair ramawa.” Marubuciyar ta ce.

“A yau mutane sun tsani Amurka ne saboda ta fi kowacce kasa karfin rinjaye a duniya. Muna tsanar wasu abubuwa da muka gani a rayuwarmu,” marubuciyar ta ce.

Tsohuwar ma’abociya akidar katolika ta addinin Kiristar ta sadaukar da rubuce-rubucenta ne a kan binciken da kamanceceniyar addini.

Tsohuwar jigo a addinin Kiristar mai shekaru 75 ta fara ne da wallafa tarihin annabi Muhammad a 1991, kamar yadda jaridar the Guardian ta wallafa. Marubuciyar ta yabawa yadda musulmai da ke Amurka suka dau rubutunta da matukar amfani a matsayinta na babbar marubuciya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng