An Bude Kasuwar Musulunci Ta Farko a Najeriya, inda Kayan Abinci Suke da Araha

An Bude Kasuwar Musulunci Ta Farko a Najeriya, inda Kayan Abinci Suke da Araha

  • Hada hadar kasuwanci ta kankama a kasuwar Musulunci ta farko da aka bude a jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
  • An rahoto cewa 'yan kasuwar na samo kayan abinci kai tsaye daga wajen manoma ne domin tabbatar da ingancinsu ga masu saye
  • An ce farashin kayan abinci sun fi sauki a kasuwar Musuluncin da aka bude, kuma Alhaji Sama'ila ya ce abin a yaba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - An fara kasuwanci gadan gadan a cikin kasuwar Musulunci ta farko da aka bude a Najeriya da ke a Ebu Alawe, Iwo, jihar Osun.

An ce babbar kungiyar Musulunci ta Amir Tawu'un da ke da hedikwata a Iwo karkashin jagorancin Sheikh Daood Imran ne suka assasa kasuwar.

Kara karanta wannan

Babban limamin Imo ya bayyana kalubalen da Musulmi ke fuskanta a Kudu maso Gabas

An bude kasuwar Musulunci ta farko a Najeriya
An samu karyewar farashin kayan abinci a kasuwar Musulunci ta farko da aka bude. Hoto: AFP
Asali: Getty Images

An bude kasuwar Musulunci a Osun

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa Musulmai a kauyen Tawu’un sun cika da farin ciki yayin da aka fara hada hada a kasuwar da aka bude a garinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasuwar wadda ta ke da nisan kilomita ɗaya daga kasuwar garin Kajola, na da kyan gani na musamman da kuma abubuwan birgewa, musamman ga Musulmi.

A wannan kasuwar, ana samo kayayyaki ne kai tsaye daga gonaki ba tare da an yi amfani da masu shiga tsakani ba wanda ke sa a samu kayan da ingancinsu.

Kayan abinci na da sauki a kasuwar

'Yan kasuwa, bayan sun sami matsugunni domin baje kolin kayayyakinsu, suna nuna farin cikinsu na rashin biyan harajin ƙungiyoyi.

Babban aikinsu kawai shi ne su kula da tsaftar kasuwar. An ce kasuwar na ci ne bayan kwanaki biyar yayin da suke samun kariya daga 'yan sa kai.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin fetur, Tinubu ya shirya kakabawa 'yan Najeriya wani sabon haraji

An ce ana sayar da mudun garri a kan N900 a kasuwar yayin da ake sayar da shi kan N1,300 a kasuwar Odo Oiri da ke kilomita biyu daga kasuwar, inji rahoton Daily Trust.

Hakazalika, a kasuwar Musuluncin ana sayar da mudun shinkafa a kan N3000 yayin da ake sayar da ita a kan N3,400 a wata kasuwar Iwo.

Akwai bukatar irin kasuwar nan a Arewa?

A zantawarmu da wani dan kasuwa, Alhaji Sama'la Nagoma, ya ce abin da aka yi a Osun na bude kasuwar Musulunci abin a yaba ne, domin zai kare Musulmai daga kayayyakin Haram.

Alhaji Sama'ila ya ce yana da tabbacin kayayyakin da aka san shari'a ta umarci Musulmi ya yi amfani da su ne za a sayar kuma za a kiyaye ka'idojin addini wajen awo da cinikayya.

Game da ko akwai bukatar samar da irin wannan kasuwar a Arewa, Alhaji Sama'ila ya ce dama ita Arewa an san kasar Musulmi ce, kusan kayan da addini ya amince ake sayarwa.

Kara karanta wannan

"A rage ciki:" Ministan Tinubu ya ce babu kudi a kasa, ya aikawa magidanta shawara

Sai dai ya ce akwai bukatar 'yan kasuwa su kauracewa tauye mudu, tsawwala kudin kaya da kuma sayar da marasa inganci domin kiyaye sharuddan addini.

Fitattun kasuwanni 10 a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa akwai wasu kasuwanni 10 na Najeriyan da suka yi fice a kasar, Afirka da duniya baki daya, inda kowacce kasuwa da abin ta ta shahara a kansa.

Kasuwannin sun hada da kasuwar Onitsha, kasuwar Kwamfiyuta ta Ikeja, kasuwar Balogun da Marina, kasuwar Ladipo ta Mushin, kasuwar Bodija ta Ibadan da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.