Fusatattun Dalibai Sun Babbake Gidan Shugaban Kwaleji a Arewa, Bayanai Sun Fito

Fusatattun Dalibai Sun Babbake Gidan Shugaban Kwaleji a Arewa, Bayanai Sun Fito

  • An shiga tashin hankali a kwalejin kmiyya da fasaha ta lafiya da ke Jega yayin da dalibai suka kona gidan shugaban makarantar
  • An rahoto cewa fusatattun daliban sun kona gidan shugaban makarantar, tare da lalata motocinsa kan karbar Naira miliyan 23
  • Wata majiya ta nuna dalibai 250 ne suka zargi kwalejin da tatsarsu Naira miliyan 23 yayin da suke shirin kammala karatunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Wasu fusatattun daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta lafiya da ke Jega a jihar Kebbi sun cinnawa gidan shugaban makarantar wuta.

An ce daliban sun kuma lalata motar shugaban makarantar, Haruna Saidu-Sauwa bayan barkewar wata zanga zanga.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Daliban kwalejin Kebbi sun kona gidan shugaban makarantarsu
Kebbi: Fusatattun daliban kwalejin Jega sun kona gidan shugaban makarantar.
Asali: Original

Dalibai sun kona gidan shugaban makaranta

Rahoton Channels TV ya nuna cewa zanga-zangar ta samo asali ne daga zargin da ake yi wa jami’an kwalejin na tatsar Naira miliyan 23 daga dalibai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce mahukuntan makarantar ne suka tatsi kudin daga dalibai 250 da ke shirin kammala digirinsu, da sunan za a yi masu wata rijista.

Da suke martani ga matakin da suke zargin makarantar ta dauka na tatsar kudinsu, daliban sun lalata motoci tare da cinnawa gidan shugaban wuta.

A cewar wata majiya daga cikin kwalejin, takaddamar ta samo asali ne daga wani sabon shirin kula da lafiya da aka bullo da shi a makarantar.

Abin da ya jawo tashin hankalin

An ce shirin na da alaka da shirin kiwon lafiyar ma'aurata da kuma kungiyar kula da lafiyar al’umma ta Najeriya inji rahoton jaridar Independent.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bugi kirji kan ilimi, NELFUND ta rabawa ɗalibai 40,000 lamunin N10bn

Majiyar ta ce kwalejin ta hade wannan shiri da sashen koyar da kiwon lafiyar muhalli domin tabbatar da cewa dalibai sun samu takardun shaidar shiga shirin.

To sai dai kuma hakan ya kai ga makarantar ta nemi karin N65,000 daga kowane dalibi na rijistar kammala karantun alhalin ta riga ta sa sun biya N30,000.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa za a yi karin bayani da zarar an samu bayanai daga ofishin ‘yan sandan Jega.

Daliban Jos sun fara zanga zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa daliban Jami’ar Jos da ke jihar Plateau sun bazama kan tituna don yin zanga-zanga kan karin kudin makaranta.

Zanga-zangar ta samu jagorancin shugabannin dalibai inda su ka bukaci hukumomin makarantar su yi gaggawar sauya wannan mataki da suka dauka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.