'Karin bayani: Mutum 3 aka harba wurin zanga-zangar ƙarin kuɗin makaranta a Kaduna

'Karin bayani: Mutum 3 aka harba wurin zanga-zangar ƙarin kuɗin makaranta a Kaduna

  • Wani dalibi a kwalejin Ilimi ta Gidan Waya da ke karamar hukumar Jama'a a jihar Kaduna ya riga mu gidan gaskiya
  • Dalibin ya rasu ne sakamakon harbinsa da bindiga da jami'in tsaro ya yi a lokacin da suka fito yin zanga-zanga a makarantar
  • Daliban makarantar sun fito yin zanga-zangar ne domin nuna kin amincewarsu da karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi a dukkan makarantuN gaba da sakandare

An bindige dalibin kwallejin Iimi na Gidan Waya da ke karamar hukumar Jema'a a jihar Kaduna har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Marigayin yana zanga-zanga ne tare da yan uwansa dalibai da suka fito domin nuna rashin amincewarsu da karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi a baya bayan nan, amma sai jami'an tsaro suka zo suna kokarin tarwatsa su.

Dalibai na zanga-zangan karin kudin makaranta a Kaduna
Dalibai na zanga-zangan karin kudin makaranta a Kwallejin Gidan Waya Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Zamfara baki ɗayansu za su bi Matawalle zuwa jam'iyyar APC, Hadimin Gwamna

Wani daya daga cikin masu zanga-zangar da ya yi magana da Daily Trust amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun fito ne su nuna kin amincewarsu da karin kudin makaranta da aka yi kawai sai suka hadu da jami'an tsaron a waje.

A cikin watan Afrilu ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da karin kudin dukkan makarantun gaba da sakandare a jihar.

KU KARANTA: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina

Kwallejin Ilimi na jihar da ke Gidan Waya na daya daga cikin manyan makarantun da abin ya shafa inda aka kara kudin makarantar zuwa N75,000, News Wire ta ruwaito.

Abin da shugaban dalibai na Kwalejin Gidan Waya ya ce game da lamarin

Shugaban kungiyar ɗaliban Nigeria reshen jihar Kaduna (NAKASS), Kwamared Tajudden Kabir ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa ana fargabar ɗalibai biyu ne suka rasu cikin uku da aka harba, LIB ta ruwaito.

"Litinin na baƙin ciki ga daliban Nijeriya da Kaduna'. A yanzu, muna taro, shugaban NANS na ƙasa da sauran jami'ai sun halarci taron. Shugaban NAKASS da jami'an NANS da dukkan shugabannin kungiyoyin ɗalibai na jihar Kaduna sun hallara', kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook.
"Muna tattaunawa game da ƙarin kuɗin makaranta da rashin tsaro a makarantun a lokacin da shugaban kungiyar dalibai na Gidan Waya ya samu kira cewa an harbi ɗalibai 3 da ke zanga-zanga, ana fargabar biyu sun mutu.
"Sakataren SUG ya isa asibitin, muna tattara bayanai domin mu tabbatar idan ɗalibin mu ya mutu da abin da ya yi sanadin harbin. Muna addu'ar Allah yasa ba a rasa rai ba a wannan gwagwarmayar. Mu cigaba da addu'a."

A baya, kun ji cewa Daliban Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, a ranar Talata sun tare babban titin zuwa gidan gwamnati a Kaduna, babban birnin jihar don yin zanga-zanga kan karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi, Channels Television ta ruwaito.

Jami'ar mallakar gwamnatin jihar ta sanar da karin kudin makaranta da kimanin 600% daga N26,000 da aka saba biya a baya.

A cewar sabon tsarin kudin makarantar da aka gabatar, yan jihar za su rika biyan N150,000 yayin da abokan karatunsu a bangaren likitanci da kimiyya za su rika biyan N170,000 zuwa sama duk shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: