Cikakken Jerin Gwamnonin CBN daga 1958 Zuwa Yau da manyan Nasarorin da Suka Samu

Cikakken Jerin Gwamnonin CBN daga 1958 Zuwa Yau da manyan Nasarorin da Suka Samu

  • Majalisar dattawa ta amince da nadin Olayemi Cardoso a matsayin gwamnan CBN a ranar Talata, 27 ga Satumba, 2023
  • Cardoso ya karbi mulki daga hannun Folashodun Adebisi Shonubi wanda ya yi aiki a matsayin mukaddashin gwamnan CBN
  • Daga Roy Fenton a 1958 zuwa Cardoso a matsayin gwamnan CBN na 14, Legit ta tattaro nasarorin da shugabannin suka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar 15 ga watan Satumba, majalisar dattawa ta amince da nadin Olayemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya na 14.

Cardoso yana da fiye da shekaru 40 na gwaninta a matsayin jagora a ma'aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu musamman a harkar sha'anin banki da kudi.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

Jerin gwamnonin bankin CBN daga 1985 zuwa yanzu
An kirkiro CBN ne a shekarar 1985 kuma shi ne ke kula da harkokin kudi na Najeriya. Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

A baya Legit Hausa ta yi karin haske kan jerin shugabannin Najeriya da gwamnonin CBN da suka yi aiki da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kirkiro CBN a shekarar 1958

An kafa babban bankin Najeriya (CBN|) a shekarar 1958. Yana tafiyar da tsarin hada-hadar kudi na Najeriya tare da tsarawa da kuma fitar da kudin kasar (Naira).

A tsawon shekarun da suka gabata, gwamnoni da dama sun shugabanci bankin CBN. Roy Pentelow Fenton, gwamna na farko, ya yi kaura ne daga kasar Ingila.

Ya rike mukamin daga 1958 zuwa 1963, lokacin da Alhaji Aliyu Mai-Bornu, dan Najeriya na farko da ya jagoranci CBN ya karbi ragamar mulki.

Gwamnonin CBN da nasarorinsu

A cikin wannan rahoto, Legit Haysa ta yi tsokaci kan irin gagarumar nasarar da kowanne daga cikin gwamnonin CBN ya samu:

1. Roy Pentelow Fenton (1958 – 1963)

Kara karanta wannan

Neman beli: Kotu ta kara hankaɗa keyar jami'in Binance zuwa kurkuku

Tsare tsaren Roy Fenton sun taimaka wajen kafa tsarin ci gaban tattalin arzikin Najeriya. Ya ba da gudunmawa wajen bunkasa tsarin hada-hadar kudi da sa CBN ya tsaya da kafafunsa.

A ranar 1 ga Yuli, 1959, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fara fitar da takardun kudin Najeriya yayin da hukumar WACB ta fitar da nata takardun, sannan aka cire sulalla.

2. Aliyu Mai-Bornu (1963 – 1967)

Aliyu Mai-Bornu ya gaji kujerar Fenton wanda ya zamo dan Najeriya na farko da ya samu mukamin. A zamaninsa ne aka kirkiro kudin Naira a 1967.

Rahoton The History Ville ya nuna cewa Sabon kudin Naira ya maye gurbin fam din Najeriya da farashin canji daga N2 kan £1 a Birtaniya da ₦1 kan $0.6 a Amurka.

Wannan ya zama babbar nasara ga ‘yancin Najeriya da kuma cin gashin kan tattalin arzki tare da nuna gagarumin sauyi a ci gaban tattalin Najeriya.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

3. Clement Nyong Isong (1967 – 1975)

Isong ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen fadada fannin noma a Najeriya. Ya aiwatar da tsare-tsare da dama da suka tada noman da fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje.

Kafin gwamnati ta yanke shawarar sauyawa daga metric zuwa decimal, an sauya sunan kudin Najeriya a ranar 1 ga watan Janairun 1973.

Babban kudin da ya kasance £1 ya daina wanzuwa kuma N1 da ta kai shilin 10, ta zama babbar kudi yayin da kobo ya zama karamin kudi, kobo 100 ya zama N1.

4. Adamu Ciroma (1975 – 1977)

Ciroma ya taimaka wajen kafa kamfanin NNPC a shekarar 1977. Kamfanin mai na NNPC ya taka rawa a fannin tattalin arziki a Najeriya kuma ya bunkasa harkar fetur da iskar gas.

A ranar 11 ga Fabrairu, 1977, CBN karkashin Ciroma ya kirkiri takardar kudi ta N20. Ita ce takardar kudi ta farko mai dauke da hoton wani dan Najeriya - Janar Murtala Ramat Muhammad (1938-1976).

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jajubo rancen $6.45bn daga bankin duniya a watanni 16

An fara amfani da takardar N20 ne a ranar cika shekara ta farko da kisan Ramat a matsayin karrama shi kuma aka ayyana shi a matsayin gwarzon kasa a ranar 1 ga Oktoba, 1978.

5. Ola Vincent (1977 – 1982)

Vincent shi ne ke kula da taron SFEM na farko a cikin 1986. SFEM ta goyi bayan 'yanci na kasuwa domin musayar kudaden waje da kuma ci gaban tattalin arziki.

An bullo da sabbin takardun kudi na N1, N5 da N10 a ranar 2 ga Yuli, 1979. Domin bambance kudin cikin sauki, an yi amfani da launuka daban-daban a kan kowacce takarda.

A lokacin da Ola Vincent ya sauka daga kujerar a 1982, ana musayar dala kan Naira a kan N0.67/$1, kamar yadda rahoton BBC yan nuna.

6. Abdulkadir Ahmed (1982 – 1993)

Ahmed ya taimaka wajen daidaita tattalin arzikin Najeriya a shekarun 1980. Ya aiwatar da tsare-tsare da suka inganta kudaden kasar da rage hauhawar farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Jarumin Kannywood, Adam Zango ya samu babban mukami, Ali Nuhu ya fito ya yi magana

A watan Afrilun 1984, an canza duk kalar takardun kudi domin dakile fataucin kudin da ya yi kamari a wancan lokacin, sannan a shekarar 1991 aka canza kwabo 50 da N1.

A shekarar 1993, lokacin mulkin Janar Sani Abacha, a hukumance farashin Naira zuwa Dala ya kai N22.05 kan kowace $1.

7. Paul Agbai Ogwuma (1993 – 1999)

Agbai ya taka muhimmiyar rawa a sake fasalin fannin banki a Najeriya. Ya sanya wasu ka'idoji da suka karfafa da kuma inganta tsarin banki.

Sakamakon fadada ayyukan tattalin arziki da samar da ingantaccen tsarin biyan kudi, an samar sabuwar takardar kudi ta N100 a Disambar 1999.

A lokacin da Paul Agbai Ogwuma ya sauka daga kujerar a 1999, ana musayar dala kan Naira a kan N93.95/$1.

8. Joseph Oladele Sanusi (1999 – 2004)

Oladele ne ya taka rawa har kasar ta fara amfani da tsarin IFEM (kasuwancin kudin kasashen waje na banki zuwa banki). An fara amfani da tsarin IFEM a Oktobar 1999.

Kara karanta wannan

EFCC ta shiga matsala da gwamnoni 16 suka maka ta a kotu, an samu bayanai

A zamaninsa na CBN ya samar da sababbin takardun kudi na N200 (Nuwambar 2000) da N500 (Afrilu 2001).

Lokacin da ya sauka daga mulki ana musayar dala kan Naira a kan N133.5/$1.

9. Charles Chukwuma Soludo (2004 – 2009)

Soludo ya jagoranci hadewar bangaren kudi na Najeriya a farkon shekarun 2000. Maimakon fiye da bankuna 80 da ake da su, sai da ya tabbatar sun koma zuwa 25 kawai a kasar.

Har ila yau, Soludo ya karɓi tsarin kudin yanar gizo a cikin 2012. Musayar kudi ta intanet ta fi arha saboda tsarinsa, wanda kuma ya ƙarfafa harkar kuɗi.

An samar da takardar kudi ta N1000 a watan Oktobar 2005. A tsakanin Fabrairu, 2007 zuwa Satumbar 2009 aka fara amfani da takardar kuɗi ta N20, N50, N10, da kuma N5 da aka yi su da leda.

A shekarar da ya hau mulki (2004) ana musayar Naira da dala a kan ₦133.5/$1, amma a shekarar 2009 da ya sauka, an koma canjin kudin kan ₦148.78/$1.

Kara karanta wannan

Sauye sauye a majalisar ministoci: Tinubu zai saki sunayen ministocin da zai kora

10. Sanusi Lamido Sanusi (2009 – 2014)

Sanusi ya bankado badakalar damfara a bangaren bankunan Najeriya a shekarar 2009. Ya kuma taimaka wajen tsaftace harkar banki ta hanyar cire gurbatattun ma’aikatan banki.

A shekarar 2010, aka sake fitar da takardar kudi ta N50 da aka yi da leda domin murnar shekaru 50 da samun samun 'yancin kan Najeriya.

A shekarar 2014 ne aka sake fasalin kudin na karshe inda aka fitar da takardar kudi ta N100 a lokacin da aka yi wani babban biki a Najeriya.

A lokacin da Sanusi Lamido Sanusi ya sauka daga kujerar a 2014, ana musayar dala kan Naira a kan N169.68/$1.

11. Sarah Alade (mukaddashiya) (2014)

An tsara shirin tattalin arziki na MTP na Najeriya da kuma shirin IMF na ma'aikata karkashin Alade. Ta rike mukamin ne na wasu 'yan watanni.

12. Godwin Emefiele (2014 – 2023)

Emefiele ya rike mukamin gwamnan CBN daga ranar 4 ga watan Yuni, 2014, har zuwa ranar 9 ga watan Yunin 2023, lokacin da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin abubuwa 63 da Gwamnatin Tinubu ta cirewa harajin VAT

A lokacin mulkinsa na farko, ya kawo tsarin shiga tsakani na kudi wanda ya hada da cika kasuwannin canjin kudade da biliyoyin daloli domin tallafawa kudin Najeriya.

Majalisar dattawa ta amince Emefiele ya ci gaba da riken mukamin gwamnan CBN na shekaru biyar a 2019. Wannan ne karon farko tun daga 1999 da wani ya taba samun tazarce.

A watan Maris 2020, babban bankin Najeriya ya daidaita farashin canji daga N307/$1 zuwa N360/$1. An samu canjin kudin zuwa N380/$ a karshen shekarar.

Najeriya ta fuskanci koma bayan tattalin arziki guda biyu cikin shekaru biyar. Na farko a shekarar 2015 zuwa 2017 sakamakon faduwar kudin danyen mai, sai kuma na biyu a tsakanin 2019 zuwa 2020 sakamakon annobar Corona.

A ranar Litinin, 25 ga Oktoba, 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da 'e-Naira' – kudin intanet da CBN ya hada wanda ke samar da wani nau’in kudin zamani na Naira.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

A watan Oktoba 2022, Emefiele ya sanar da shirin babban bankin na sake fasali tare da rarraba sababbin takardun kudi na N200, N500 da N1000.

A lokacin da Godwin Emefiele ya sauka daga kujerar a 2023, ana musayar dala kan Naira a kan N638.7/$1.

14. Olayemi Cardoso (2023 – zuwa yau)

Yemi Cardoso shi ne gwamnan babban bankin CBN a yanzu, bayan da ya dare kujerar a ranar 22 ga Satumba, 2023, inji rahoton ThisDay.

Karkashin jagorancin Cardoso na shekara guda, CBN ya aiwatar da wasu matakai da suka inganta daidaiton harkokin kudi da kuma kokarin daidaita darajar kudin kasar.

Haka kuma, CBN a karkashin Cardoso ya samu damar kawo tsare tsare da suka taimaka wajen yakar hauhawar farashin kayayyaki da ya addabi al’ummar kasar tsawon shekaru.

Sakamakon karyewar darajar Naira da aka samu, matakan da CBN ya dauka ba su yi tasiri wajen dakile hauhawar farashin kayayyakin ba.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Mafi girman canjin dalar Amurka zuwa Naira ya kasance a ranar 26 ga Satumba, 2024 inda dalar Amurka daya ta kai 1,692.3900 a kudin Najeriya.

Emefiele ya sauya Naira ba Buhari ba

A wani labarin, mun ruwaito cewa an ci gaba da sauraron shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan sauya fasalin Naira a shekarar 2022.

Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Edward Adamu, ya ce Emefiele ya sauya fasalin kuɗin Naira a 2022 ba da amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.