'Akwai matsala': Yadda Malami 1 Ke Koyar da Daruruwan Dalibai a Makarantun Gwamnati
- Rahotanni sun ce malami daya ne kacal ko kayar da sama da dalibai 165 a wata makarantar firamare ta Okugbe, Ikpide-irri
- Mazauna Ikpide-irri da ke karamar hukumar Isoko ta Kudu a Delta sun ce gwamnati ta ware su daga samun romon dimokuradiyya
- Masana na ganin cewa yawan dalibai da ya wuce kima a aji daya na zama abin wahala ga malami wajen koyar da daliban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - Mazauna Ikpide-irri da ke karamar hukumar Isoko ta Kudu a jihar Delta, sun nuna rashin jin dadinsu game da rikon sakainar kashi da gwamnati ke yiwa yankinsu.
Bacin ran nasu ba zai rasa nasaba da tabarbarewar ilimi ba, inda aka ce malami daya ne ke koyar da dalibai 170 a makarantar firamare ta Okugbe, Ikpide-irri.
Tabarbarewar rayuwa a garin Ikpide-irri
Jaridar Leadership ta kuma rahoto cewa mazauna yankin sun nuna takaicinsu kan yadda suke tafiya har jihar Bayelsa domin neman lafiyarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar da ta gabata ne al’ummar yankin suka rasa wata mata mai juna biyu a lokacin da take nakuda bayan an kaita garin Kaiama da ke Bayelsa inda suke zuwa neman lafiya.
\Ikpide-irri al’umma ce ta noma, wadda ta kware wajen noman doya, ayaba, barkono da rogo domin tabbatar da wadatar abinci a jihar.
Ikpide-irri sun kain koke wajen gwamnati
Wata kungiya ta CIID ta ziyarci shugaban karamar hukumar Isoko ta Kudu, Kwamared Friday Warri inda suka roki gwamnati ta kai masu romon dimokuradiyya.
A jawabin da Kwamared Obruozie Odiuzou ya gabatar a madadin CIID, al’ummar yankin sun koka kan rashin malamai a makarantun firamare da sauran bukatun rayuwa.
Shugaban karamar hukumar, Kwamared Friday Warri, ya bayyana kaduwarsa a wata ziyarar bazata da ya kai makarantar domin tantance abubuwan more rayuwa da suka lalace a yankin.
Yawan dalibai a makarantun gwamnati
A zantawar Legit Hausa da wani shugaba a makarantar firamare, Nura Lawal Mailafia ya ce yawan dalibai a cikin ajujuwan makarantun gwamnati na kawo nakasu ga karatu.
Nura Mailafia ya ce ana samun sama da dalibai 70 a wasu ajujuwan, wanda hakan ke ba malamai ciwon kai wajen ganin sun koyar da daliban karatu ta yadda za su gane.
"Wannan ne ya sa iyaye da dama ke mayar da 'ya'yansu makarantun kudi inda za ka tarar da dalibai 20 zuwa 30 a aji daya, wanda malami ke iya tafiyar da su."
- A cewar Malam Nura.
Yadda za a rika ladabtar da dalibai
A wani labarin, mun ruwaito cewa masana sun soki ladabtar da yara dalibai ta hanyar yi masu dukan tsiya, inda suka ce akwai bukatar daukar wasu matakai na ladabtarwa.
Wannan na zuwa ne bayan wasu malamai a makarantar Al-Azhar sun lakadawa wani dalibi dukan tsiya har sai da ya rasa ransa a Zaria da ke jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng