Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ke Noman Doya a Cikin Buhunna Ba a Gona Ba

Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ke Noman Doya a Cikin Buhunna Ba a Gona Ba

  • Wani dan Najeriya ya baje kolin yadda yake noman amfanin gonarsa ta hanyar dasa su a cikin buhuhuna maimakon cikin kasa
  • A wani bidiyo da ya shahara, mutumin ya bayyana irin cigaban da ya samu bayan dasa shukokin 4000 na doya a kan wani fili
  • Ya karfafa wa masu kallonsa gwiwa da su gwada salon nomansa kamar yadda da ya nuna mutum zai iya noman doya sau biyu a shekara

Legit.ng ta samo bidiyon wani dan Najeriya ya shiga harkar noma ta wata hanyar da ba a saba gani ba.

Mutumin da ba a bayyana ko wanene shi ba, a bidiyon da Ayo Ojeniyi ya yada a Facebook, ya nuna yadda ya shuka dashen doya 4000 a wani fili a jihar Anambra.

Yana shuka amfanin gonarsa a cikin buhuhuwan siminti. A cikin bidiyon, ya karfafawa mutane su gwada irin wannan tsarin nashi. Ya ci gaba da bayyana cewa mutum na iya shuka doya sau biyu a shekara da wannan dabarar noma kuma ba a bukatar babban fili.

KU KARANTA: Gwamnan Neja ya koka kan yadda 'yan bindiga suka hana karatu da noma a jiharsa

Bidiyon yadda wani dan Najeriya ke noman doya a cikin buhunna ba a gona ba
Yadda wani mutum ya shuka doya a cikin buhunnan siminti | Hoto: Ayo Ojeniyi
Asali: Facebook

A cikin bidiyon, tuni shukar doyar har ta riga ta fara toho, kalli bidiyon a kasa.

Mutane a kafar Facebook sun yi martani kan wannan salon noman nasa

Emeka Ugwuowo ya ce:

"Tare da tsari mai kyau da ci gaba irin wannan, zamu iya kayar da yunwa ta hanyar noma wanda zai bada tabbacin wadataccen abinci mai inganci.
"Idan abinci yana da araha kuma akwai kyawawan masaukai masu sauki, aikata laifi zai ragu da 50% cikin 100% a cikin kankanin lokaci."

Ayoola Akinkunmi Olamide ya rubuta:

"Ina gwada wannan a gidana a halin yanzu. Na shuka 'yan kadan a wani fili da kuma wasu a cikin buhu."

Hayourdaejee Kunle Suraji ya ce:

'' Ina son ganin karshen wannan sabon tsari na dashen doya."

KU KARANTA: Mu Tagwaye Ne: Koriya Ta Arewa Na Bukatar Kara Dankon Alaka da Najeriya

A wani labarin, Rahotanni daga kasar Indiya sun bayyana cewa, wani mutum da ya fi kowa yawan iyalai a duniya ya mutu sakamakon wata jinya da yayi na ciwon suga, Sky News ta ruwaito.

Mutumin, wanda aka bayyana shi a matsayin wanda ya fi kowa yawan iyalai ya rayu cikin farin ciki tare da mata, 'ya'ya da tarin jikoko masu yawa. An ruwato cewa, mutumin yana da mata 39 da 'ya'ya 89 da kuma jikoki masu yawan gaske.

Ko ya ya rayuwar gidansa za ta kasance? Legit.ng Hausa ta tattaro wasu hotuna da ta samo daga BBC dake nuna yadda rayuwa take a gidan mutumin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel