Ana Shigo da Makamai Najeriya, Hukumar NFIU Ta Fadi Kasar da Ake Kawo Kayan Yaki
- Hukumar tattara bayanan sirri kan sha'anin kuɗi ta nuna damuwa kan yadda makamai ke kwararowa cikin Najeriya
- Shugabar NFIU, Hafsat Bakari ta bayyana cewa ta'addanci na ta'azzara a Najeriya ne saboda shigowar makamai daga Libya
- Domin samun nasara a yaki da 'yan bindiga a kasar nan, Bakari ta ce Najeriya na bukatar taimako daga kasashen duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar tattara bayanan sirri kan sha'anin kuɗi (NFIU), ta ce ana shigo da makamai Najeriya daga kasar Libya wanda ke ta'azzara kalubalen tsaro.
Hukumar NFIU ta ce akwai bukatar Najeriya ta sauya salo a yayin da take kokarin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin Sahel.
"Makamai na kwarorowa Najeriya" - NFIU
Jaridar Daily Trust ta rahoto NFIU ta ce akwai bukatar a daidaita dabarun yaki da safarar kudi da ta'addanci (AML/CFT/CPEF).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar tattara bayanan sirrin ta ce za a iya cimma hakan ne ta hanyar shigar da kamfanoni masu zaman kansu da ke a fannin.
Shugabar hukumar NFIU, Hafsat Abubakar Bakari, ta bayyana hakan a lokacin da ta jagoranci tawagan zuwa taron cibiyar CPIE a birnin Washington D.C, inji rahoton Guardian.
"Najeriya na fuskantar wani gagarumin rikicin cikin gida na 'yan bindiga da ke kara ta'azzara sakamakon kwararowar makamai daga Libya, wanda ya zama abin damuwa."
- A cewar Hafsat Bakari.
"Najeriya na bukatar kasashen duniya" - NFIU
A cikin wata sanarwa da shugaban watsa labarai na NFIU, Sani Tukur ya fitar, an ruwaito Hafsat Bakari ta ce shigowar makaman ya ta ta’azzara matsalar tsaron Najeriya.
Shugabar hukumar tattara bayanan sirri kan sha'anin kuɗin wadda ta yi kira da a dauki matakin da zai kawo karshen ta'addanci gaba daya a Najeriya ba wai na dan wani lokaci ba.
Ta kara da cewa Najeriya na bukatar taimakon kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci da kuma takaita safarar kudi a yankin Sahel da yankin tafkin Chadi.
An gano yadda ake shigo da makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce ta gano yadda ake shigo da makamai Najeriya ta yankin tashar ruwan Onne da ke jihar Ribas.
Shugaban hukumar kwastam na kasa, Bashir Adeniyi wanda ya bayyana haka ya ce shigo da makamai da ake yi ta yankin na barazana ga tsaron Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng