Rahoton 2025: ABU, UI Sun Shiga Gaba a Jerin Manyan Jami'o'in Gwamnatin Tarayya

Rahoton 2025: ABU, UI Sun Shiga Gaba a Jerin Manyan Jami'o'in Gwamnatin Tarayya

  • An bayyana jami'ar Covenant a matsayin mafi kyawun jami'a a Najeriya, bisa rahoton da Times Higher Education (THE) ta fitar
  • Sai dai jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke garin Zariya, ta zama ta daya a jerin manyan jami’o’in gwamnatin tarayya na kasar nan
  • An rahoton cewa jami'o'i 44 daga cikin 264 da ake da su a Najeriya sun fito a cikin kididdigar da THE ta fitar a matakin jami'o'in duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna – Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Kaduna, ta yi nasarar zama ta daya a jerin jami’o’in gwamnatin tarayya mafi kyawu a Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, ABU ta fito ne a matsayin ta daya a rahoton kididdigar manyan jami'o'in duniya da Times Higher Education (THE) ta fitar.

Kara karanta wannan

Atiku ko Wike? Shugabanni sun bayyana wanda ya haddasa rikicin da ya mamaye PDP

ABU da UI sun shiga gaba a jerin manyan jami'o'in gwamnatin tarayya a Najeriya
ABU ta ciri tuta a jerin manyan jami'o'in gwamnatin tarayyar Najeriya a 2025. Hoto: PeopleImages
Asali: Getty Images

Akwai fiye da jami'o'in tarayya 10 a cikin jerin manyan jami'o'in da THE ta fitar a shafinta na intanet, kuma jami'o'in sun fito daga jihohi 9 na kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duba jerin manyan jami'o'in a kasa:

1. Jami'ar Ahmadu Bello (ABU)

Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) jami'ar bincike tarayya ce da ke Zaria, jihar Kaduna. An bude ta a shekarar 1962 a matsayin Jami'ar Arewacin Najeriya

2. Jami'ar Ibadan (UI)

Jami'ar Ibadan (UI) ita ma jami'ar bincike ce ta al'umma da ke a jihar Oyo.

Jami'ar ta kasance kwalejin Jami'ar Landan. A shekarar 1948 ne aka mayar da ita kwalejin jami'ar Ibadan, daya daga cikin kwalejoji masu yawa da ke cikin jami'ar Landan.

3. Jami'ar Legas (UNILAG)

Jami'ar Legas (UNILAG) jami'ar bincike ce ta jama'a da ke Legas, wacce aka kafa a 1962.

Kara karanta wannan

Jami'an gwamnati sun nemi cin hancin N5000 a filin jirgin sama? FAAN ta magantu

UNILAG na ɗaya daga cikin jami'o'in ƙarni na farko a Najeriya.

4. Jami'ar Bayero, Kano (BUK)

An kafa BUK ne a shekarar 1975 lokacin da aka canza sunanta daga kwalejin jami’ar Bayero kuma aka daga darajarta daga kwalejin Jami’a zuwa ciakkiyar jami’a.

Jami'ar Bayero (BU) Ita ce jami'a ta farko a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

5. Jami'ar fasaha ta tarayya, Akure

Jami'ar fasaha ta tarayya, Akure (FUTA) jami'a ce mallakar gwamnatin tarayya da ke Akure, jihar Ondo.

An kafa ta ne a 1981 bisa kudurin gwamnatin tarayya na samar da jami'o'in da za su rika yaye daliban da ke da kwarewa kan fasaha da aiwatarwa.

6. Jami'ar fasaha ta tarayya, Minna

Jami'ar fasaha ta tarayya, Minna (FUTMinna) jami'a ce mallakar gwamnatin tarayya da ke garin Minna.

FUT Minna ta kware a fannin ilimin kere-kere kuma ta na ba da digiri na farko da na biyu a fannonin fasaha daban-daban.

Kara karanta wannan

Ba a warware batun Ganduje ba, kotu ta yi hukunci kan kujerar shugaban jam'iyyar LP

7. Jami'ar Benin (UNIBEN)

Jami'ar Benin (UNIBEN) jami'ar bincike ce ta jama'a da ke cikin garin Benin, jihar Edo.

UNIBEN tana cikin jami'o'in da gwamnatin tarayya ta gina kuma aka kafa ta a 1970.

8. Jami'ar Ilorin UNILORIN)

Jami'ar Ilorin (UNILORIN) jami'ar bincike ce ta gwamnatin tarayya da ke a Ilorin, jihar Kwara.

Jami'ar Ilorin ita ce jami'a mafi girma a Najeriya kuma daya daga cikin mafi girma a Afirka ta fuskar girman kasa.

9. Jami'ar Najeriya (UNN)

Jami'ar Najeriya, wacce aka fi sani da UNN, jami'a ce ta tarayya da ke Nsukka, jihar Enugu da ke a Gabashin Najeriya.

An kafa makarantar ne a shekarar 1955 a karkashin marigayi Nnamdi Azikiwe, shugaban Najeriya na farko bayan samun 'yancin kai.

10. Jami'ar noma ta tarayya, Abeokuta

Jami’ar noma ta tarayya da ke Abeokuta (FUNAAB) na daya daga cikin manyan jami'o'in da gwamnatin tarayyar Najeriya ke gudanarwa.

Gwamnatin tarayya ta kafa FUNAAB ne a ranar 1 ga Janairu, 1988, lokacin da aka rusa wasu jami'o'in fasaha guda hudu da aka taba hade su a 1984.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

Jami'o'in Najeriya 10 mafi daraja

A wani rahoton, mun ruwaito cewa Jami'ar Covenant ta sake rike kambunta karo na biyu na jami'a mafi daraja a Nijeriya bayan doke jami'ar Ibadan da jami'ar FUTA.

Manyan jami'o'i 15 na Nijeriya sun fito ne daga Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya bisa kididdigar THE.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.