Jerin Jami'o'in Gwamnatin Tarayya Da Suka Kara Kudin Makaranta

Jerin Jami'o'in Gwamnatin Tarayya Da Suka Kara Kudin Makaranta

Biyo bayan gazawar kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU wajen tilastawa gwamnatin tarayya karawa jami'o'i kudi, wasu jami'o'in sun nemawa kansu sauki ta hanyar kara farashin kudin makaranta.

Jami'an gwamnatin tarayya da dama sun yi karin ninkin ba ninki na kudin da dalibai zasu biya.

Ga jerin jami'o'in da suka kara kudin makaranta:

Jami'ar Tarayya, Dutse

Jami'ar tarayya dake Dutse ta sanar da karin kudin makaranta da 200% a sabon kakar 2022/2023 da za'a shiga.

Jami'ar ta sanar da hakan a jawabin da ta fitar a Disamba, 2022.

Domin saukakewa daliban, jami'ar ta ce mutum zai iya biyan kashi 60% a zangon farko, sannan ya biya kashi 40% a zango na biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojojin Najeriya Sun Halaka Babban Ɗan Ta'adda da Wasu Mayaƙa Sama da 40 a Arewa

Jami'ar Maidugrui (UNIMAID)

Jami'ar Maiduguri ta ce ta kara kudin makaranta saboda hauhwar farashin kayayyaki a fadin kasar.

Ga jerin karin da UniMaid tayi:

Sabbin daliban Likitanci- N252,500;

Sabbin daliban Nursing - N136,500;

Daliban Anatomy - N162,500;

Daliban Physiotherapy - N131,500;

Tsaffin daliban tsangayar kimiya kuwa - Tsakanin N112,000 da N258,000

Unimaid
Jerin Jami'o'in Gwamnatin Tarayya Da Suka Kara Kudin Makaranta
Asali: UGC

Jami'ar tarayya, Lafia (FULafia)

Jami'ar tarayya dake Lafia, jihar Nasarawa ta kara farashin kudin rijistan dalibai kuwa har N150,000.

Daga yanzu daliban karatun Likitanci zasu biya N150,000 kudin rijista kadai.

Jami'ar Uyo (UniUyo)

A baya daliban UniUyo na biyan N50,000. Amma yanzu an ruwaito cewa an kara kudin zuwa N100,000.

Daliban dake karatun likitanci kuwa zasu biya N107,750, Yayinda daliban tsangayar ilimi zasu biya N75,750.

Jami'ar Noma ta Michael Okpara , Umudike

Jami'ar noman Michael Okpara dake Umudike ta bi sahun jami'o'i wajen kara farashin kudin makaranta. Ta daura laifin kan tashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Inconclusive: Sanata Aishatu Binani Ta Maida Martani Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Adamawa

Jami'ar ta sanar da hakan a Disamba 2022.

Jami'ar Ibadan Da Lagos Sun Sha Gaban Jami'oin NIgeria A wani Bincike Da Aka Gudanar

A wani labari, Mujallar Times Higher Education ta fitar da jadawalin makarantun da suka fi kowanne a duniya.

Jaddawalin dya ƙunshi jami'o'i 1,799 a cikin ƙasashe da yankuna 104 kuma jami'oin Najeriya 10 sun samu shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel