Jami'an Gwamnati Sun Nemi Cin Hancin N5000 a Filin Jirgin Sama? FAAN Ta Magantu

Jami'an Gwamnati Sun Nemi Cin Hancin N5000 a Filin Jirgin Sama? FAAN Ta Magantu

  • Hukumar FAAN ta yi martani kan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya inda wata mata ta zargi jami'anta da neman cin hanci da rashawa
  • A cikin bidiyon an ga wasu jami'an filin jirgin Murtala Mohammed suna sa'insa da matar inda ta ce sun ci zarafinta kuma sun nemi N5000
  • Sai dai hukumar FAAN ta ce duk abin da matar ta fada a bidiyon ba gaskiya ba ne har ta bayyana gaskiyar abin da ya faru game da batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Hukumar FAAN ta mayar da martani kan wani faifan bidiyo da aka nuna wasu jami’anta suna cacar baki da wata mata a filin jirgin sama na Murtala Mohammed.

Kara karanta wannan

'Zancen bur inji tusa', APC ta fadi abin da zai faru a hadakar Kwankwaso da Peter Obi

A cikin faifan bidiyon da ke yawo a intanet, matar da ba a tantance ko wacece ba ta zargi ma’aikatan filin jirgin da neman cin hancin N5000 domin tantance jakunkunanta.

Hukumar FAAN ta yi magana kan bidiyon matar da ta zargi jami'anta da cin hanci da rashawa
FAAN ta yi martani kan rigimar da aka yi tsakanin wata mata da jami'an filin jirgin Legas. Hoto: @FAAN_Official
Asali: Facebook

Ma'aikatan FAAN na neman cin hanci?

A bidiyon da TVC News ta wallafa a shafinta na YouTube, an dai ji matar tana ihu tana cewa ita fasinja ce kuma tana mamakin dalilin da ya sa jami’ai ke neman cin hancin N5000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon dai ya janyo martani daga 'yan Najeriya inda da dama suka yi ta caccakar ma'aikatan filin jirgin tare da zarginsu da karbar cin hanci da rashawa.

FAAN ta yi martani ga bidiyon matar

Sai dai a wata sanarwa da aka fitar a safiyar yau 8 ga watan Oktoba, FAAN ta ce abubuwan da matar ke fada a bidiyon ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

NAHCON: Ana fargabar kudin aikin Hajji zai koma N10m a Najeriya, an gano dalili

FAAN ta ce matar da ke cikin bidyon ba fasinja ba ce, jami’ar daukar kaya ce da ke gudanar da ayyuka ba bisa ka’ida ba a filin jirgin.

"Ta ki biyan kudin da aka gindaya na tantance kaya kuma ta nuna wata iriyar dabi'a da ba za a lamunta da ita ba, ta lalata kayan aiki tare da tauye albarkatunmu.
"Za mu kuma fayyace cewa babu wani nau'i na cin zarafi da ma'aikatan FAAN suka yi, haka nan babu wani batu na neman cin hanci yayin faruwar lamarin."

FAAN ta yi kira ga daukacin jami’an dakon kaya da su rika gudanar da ayyukansu a wuraren da aka kebe da yin amfani da ababen hawa da suka dace tare da kuma biyan haraji.

Kalli bidiyon a kasa:

An hari jirgi bayan sauka Legas

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun farmakin jirgin saman kasar Morocco yayin ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun fatattaki masu sallar juma'a a wasu masallatai a Katsina

An rahoto cewa 'yan bindigar sun kwashi kayayyaki a bangaren da ake ajiye kayayyaki na jirgin jim kadan bayan saukarsa filin jirgin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.