Karya dokar FG: FAAN ta yi 'Ala-wadai' da hallayyar Abdulaziz Yari a filin jirgin Kano

Karya dokar FG: FAAN ta yi 'Ala-wadai' da hallayyar Abdulaziz Yari a filin jirgin Kano

Hukumar kula da filayen jirgin sama mallakar gwamnatin Najeriya (FAAN) ta yi 'Alla-wadai' da halayyar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya nuna a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu da ke birnin Kano.

Ana zargin tsohon gwamna Yari da karya dokar da gwamnatin tarayya ta saka bayan bude filayen jirgi domin cigaba da jigilar fasinjoji a iya cikin Najeriya sakamakon sassauta dokar kulle a mataki na biyu.

Tun kafin a bude filayen jirgin sama, gwamnatin tarayya ta sanar da jerin wasu matakai da fasinjoji da kamfanonin jirage zasu yi wa biyayya domin dakile yaduwar annobar korona.

A cikin sanarwar da FG ta fitar, ta bakin ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika, ta ce babu batun wasu shafaffu da mai ko manyan mutane (VIPs) wajen tabbatar da cewa an yi aiki da dokoki da shawarwarin gwamnati a kan kowanne fasinja.

A cikin wani sako da FAAN ta wallafa ranar Laraba a shafinta na Tuwita, ta yi 'tir' da halayyar Yari ta wofantar da dokar FG wacce ta bukataci a yi aiki da ita a kan kowanne fasinja a filin jirgin sama na kasa da aka bude.

Karya dokar FG: FAAN ta yi 'Ala-wadai' da hallayyar Abdulaziz Yari a filin jirgin Kano
Abdulaziz Yari
Asali: Twitter

"Hukumar FAAN tana mai yin Alla-Wadai da halayyar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alh. Abdulazai Yari, na karya dokoki da matakan dakile yaduwar annobar korona a filin jirgin sama na Kano a ranar Asabar, 11 ga watan Yuli, 2020," kamar yadda FAAN ta wallafa a shafinta na Tuwita (@FAAN_Official).

Hukumar FAAN ta cigaba da cewa; "Yari ya ki yin biyayya ga dokoki da matakan da gwamnatin tarayya ta saka ta hannun kwamitin kar ta kwana da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar korona (PTF).

DUBA WANNAN: Nan bada dadewa ba za a rasa ma su karfin gwuiwar yaki da cin hanci - Osinbajo

"Ya yi amfani da karfi wajen ture jami'in FAAN a yayin da ya matsa a kan cewa sai an yi wa jakar kayan Yari feshin maganin da ke kashe kananan kwayoyin cuta.

"Tsohon gwamnan ya ture jami'in sashen kula da tsaftar muhalli a FAAN tare da yi masa tunin ya sani cewa shi babban mutum ne (VIP).

"Hakan ba daidai bane, ba halin girma bane, saboda halayyarsa za ta iya saka rayuwar sauran fasinjoji cikin hatsari. Ba zamu yarda da irin wannan halayya ba, a saboda haka mun mika maganar zuwa sama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel