Kwace Kadarori: An Samu Koma baya a Shari'ar Tsohuwar Minista da EFCC
- Tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke ta gamu da koma baya a shari'ar da take yi da hukumar yaki da rashawa ta EFCC
- Diezani Alison-Madueke ya nemi wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta hana EFCC sayarwa jama'a kadarorinta da aka kwace
- A yau Litinin ne aka sanya kotun za ta yi zama kan wannan shari'ar, sai dai kuma an ce alkalin kotun, Inyang Ekwo bai samu zaman ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An samu koma baya a karar da tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke ta shigar na dakatar da hukumar EFCC daga kwace mata kadarori.
An rahoto cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da aka shigar da karar gabanta ba ta yi zama ba a ranar Litin, lamarin da ya jawo tsaiko a shari'ar.
Shari'ar Diezani da EFCC ta samu cikas
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an shirya sauraron shari'ar wadda ke gaban Mai shari'a Inyang Ekwo a yau Litinin. Sai dai kuma kotun ba ta yi zama a yau din ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Mai shari'a Ekwo ya na halartar wani taron karawa juna sani a Cibiyar Shari’a ta kasa (NJI) da ke Abuja a halin yanzu, dalilin dage zaman kotun na yau.
Daga baya ne aka bayyana dage sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga Nuwamba.
Ministar Jonathan ta yi karar EFCC
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tsohuwar ministar ta bakin lauyanta, Cif Mike Ozekhome, SAN, ta kai karar EFCC kan kadarorinta.
Tsohuwar ministar a cikin karar ta bukaci a kara wa’adin lokacin neman izinin shigar da kara domin a yi watsi da kudurin EFCC na baje kolin kadarorinta.
Alison-Madueke ta yi ikirarin cewa ba a ba ta cikakken damar kare kanta ba a lokacin da aka ba EFCC izinin cefanar da kadarorinta don haka ne take neman kotu ta yi adalci.
Diezani ta roki alfarmar Tinubu?
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke ta karyata cewa ta roki alfarmar shugaba Bola Tinubu na ya bar ta ta dawo Najeriya.
Alison-Madueke da ta tsere zuwa Birtaniya a shekarar 2015 bayan da aka tuhume ta da cin hanci da rashawa ta ce karya ake yi mata, ba ta nemi alfarmar Tinubu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng