Yajin Aiki a Jami'a: Gwamnan Gombe Ya Dauki Matakin Sasantawa da Kungiyoyin Kwadago
- Gwamnatin Gombe ta kafa kwamiti da zai tattauna da kungiyoyin malamai da ma'aikatan jami'ar jihar ta GSU bayan shigar wasu yajin aiki
- Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Njodi ya ce mataimakin gwamnan jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau zai jagoranci kwamitin
- Kwamitin zai duba yarjejeniyar gwamnati da kungiyoyin ta 2021 da ta kunshi kara kudin gudanarwar jami'ar, biyan alawus na EAA da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kafa babban kwamiti da zai nemi sasantawa da ASUU, SSANU, NASU da NAAT na reshen jami'ar Gombe (GSU).
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Njodi ya fitar ta ce kwamitin zai kasance karkashin mataimakin gwamnan jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau.
Yajin aiki: Gwamnan Gombe ya kafa kwamiti
Ya kuma ce an dorawa kwamitin da ya kunshi wasu manyan jami’an gwamnati alhakin tattaunawa kan bukatun da kungiyoyin suka gabatar, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Ibrahim Njodi ya kuma ce kwamitin zai warware dukkan matsalolin kungiyoyin ta hanyar tattaunawa domin tabbatar da daidaiton ayyukan ilimi a jami'ar GSU.
Sauran 'yan kwamitin sun hada da kwamishinoni daga ma'aikatun kananan hukumomi, ilimi, kudi da kuma shugaban hukumar IRS da babban mai binciken kudi na jihar.
Akanta-Janar na Gombe, babban sakatare, ofishin bunkasa aikin gwamnati, shugaba da mataimakinsa na kungiyar ALGON na daga cikin 'yan kwamitin.
Za a shawo kan kungiyoyin jami'ar GSU
Tribune ta rahoto Farfesa Njodi, wanda ya sanar da amincewar gwamnan ya bayyana ayyukan kungiyar da suka hada da; duba bukatun kungiyoyin malamai da ma'aikatan jami'ar.
Za su duba yarjejeniyar da akaa cimmawa a 2021 wanda ta kunshi kara kudin gudanarwar jami'ar GSU da biyan alawus na EAA.
Yarjejeniyar ta hada da batun kafa asusun tallafawa ma'aikatan da ke son zuwa karo karatu.
Akwai kuma wasu batutuwan da ba a warware su ba, kamar gyaran mafi karancin albashi na N30,000 da kuma karawa ma'aikatan ilimi albashi na kaso kashi 35 da kashi 25.
Akwai maganar sabunta alawus-alawus na DTA, aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000 da sakin jadawalin tsarin kwamitin ziyara zuwa jami'ar na 2023.
GSU: ASUU ta shiga yajin aiki a Gombe
Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar malaman jami'a ta kasa (ASUU) reshen jami'ar jihar Gombe (GSU) ta sanar da tsunduma yajin aiki.
Sanarwar da shugaban ASUU a jami'ar, Dakta Salihu Sulaiman Jauro ya fitar ta nuna cewa sun shiga yajin aikin ne domin kare muradunsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng