Fitattun ‘Yan Siyasar Kudancin Najeriya da Za Su Iya Kalubalantar Tinubu a 2027
- Manyan 'yan siyasar Najeriya na ci gaba da wasa wukarsu da kuma kulla ɗamari domin tunkarar babban zaben 2027 da ke tafe
- Akwai 'yan siyasa daga jam'iyyun adawa da ake sa ran za su kalubalanci shugaba Bola Tinubu idan ya yi yunkurin neman tazarce
- Har yanzu dai masana na ganin cewa Bola Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne shi ne jagaba a siyasar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - 'Yan siyasa a Najeriya sun fara daura damarar tunkarar zaben shugaban kasa na 2027 da ke tafe.
Ana tunani Bola Tinubu, wanda shi ne shugaban kasar Najeriya a yanzu zai nemi tazarce a 2027 a lokacin zai kai shekaru 75 a duniya.
A wannan rahoton, Legit.ng ta zayyano bayanan wasu manyan 'yan sandar Kudancin Najeriya da za su iya kararawa da Tinubu a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan siyasar Kudu da za su iya karawa da Tinubu
1. Peter Obi
Jagoran jam'iyyar Labour (LP), Peter Obi ya kasance dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ya gabata.
A shekarar 2019, Peter Obi ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a neman takarar zaben shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP amma suka sha kasa.
Dan shekaru 63, Peter Obi ya yi fice musamman a wajen matasa bayan hada gangamin 'yan Obidient'.
Ana ganin Peter Obi zai iya ba da Bola Tinubu matsala a 2027 saboda Kudu maso Gabas za ta so samun shugaban kasa, kasancewar ba ta yi ba tun daga 1999.
2. Nysom Wike
Nysom Wike wanda shi ne ministan babban birnin tarayya Abuja, cikakken dan jam'iyyar PDP ne.
Wike mai shekaru 56 na daya daga cikin manyan 'yan siyasar Kudancin Najeriya sai dai ya taba cewa ba zai gwabza da Tinubu ba.
Duk da cewa ana ganin kamar yana biyayya ga Tinubu a yanzu amma ana hasashen zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
3. Adewole Adebayo
Barista Adebayo ya kasance mai sharhi kan harkokin al'umma wanda kuma ke ba sa shawarwari kan yanayin siyasa da makomar Najeriya.
Adebayo, wanda dan asalin jihar Ondo ne ya nemi takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar SDP a zaben 2023.
Bayan gaza samun nasara a 2023, an ce Adebayo ya shirya tsaf domin tunkarar zaben 2027.
4. Dan Nwanyanwu
Dan Nwanyanwu ya kasance dan asalin Imo ne kuma shi ne shugaban jam'iyyar Zenith Labour (ZLP).
Ya rike shugaban jam'iyyar Labour (LP) daga shekarar 2004 zuwa 2014 a Najeriya.
Nwanyanwu shi ne dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam'iyyar ZLP amma bai samu kuri'u masu yawa ba.
An fara tallar Tinubu gabanin 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa allunan da ke tallata shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin zaɓen 2027 sun fara bayyana a babban birnin tarayya Abuja.
Allunan da ke ɗauke da hoton Tinubu da uwargidan gidansa Remi Tinubu sun nuna aniyar shugaban ƙasan na neman tazarce a zaben 2027 da ke tafe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng