Hukunci: Kotu Ta Takawa Hukumar VIO Burki kan Kwace Motoci da Cin Tarar Direbobi

Hukunci: Kotu Ta Takawa Hukumar VIO Burki kan Kwace Motoci da Cin Tarar Direbobi

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin Mai shari'a Evelyn Maha ta haramta wasu ayyukan da hukumar VIO ke gudanarwa
  • Kotun ta yi hukunci ne a kan karar da wani lauya, Abubakar Marshal ya shigar inda ya kalubalanci halascin ayyukan hukumar VIO
  • Kotun ta haramta wasu ayyukan hukumar VIO domin kare hakkokin masu ababen hawa musamman dangane da cin tarar direbobi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramtawa jami'an hukumar VIO dakatar da ababen hawa, kwace masu motoci ko cin tarar direbobin.

Ana ganin wannan sabon hukuncin da kotun ta yi zai kawo babban sauyi ga yadda hukumar VIO ke gudanar da ayyukanta a kan titunan kasar nan.

Kara karanta wannan

An samu karin bayani kan yadda ICPC ta kwato N13bn da aka handame a wata 1

Kotu ta yi hukuncin ko haramcin wasu ayyukan jami'an hukumar VIO
Kotu ta haramtawa jami'an hukumar VIO kwacewa ko cin tarar masu ababen hawa. Hoto: Directorate of Road Traffic Services - FCT VIO. Abuja
Asali: Facebook

Kotu ta takawa jami'an VIO burki

A wani rahoton BBC Hausa, Mai shari'a Evelyn Maha ta yanke hukuncin ne bayan wani lauya, Abubakar Marshal ya shigar da hukumar VIO kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Abubakar ya kalubalanci halascin ayyukan jami'an hukumar VIO a gaban kotun, inda ya ce suna tauye hakkokin masu ababen hawa.

A hukuncin da Mai shari'a Evelyn ta yanke, ta ce VIO ba ta da hurumin kwace ababen hawa ko kuma cin tarar direbobi balle a yi maganar tare su a kan hanya.

Kotu: 'Hukumar VIO ba ta da hurumi'

Mai shari'a Evelyn ta jaddada cewa:

"Babu wata doka da ta sahalewa wanda ake kara na hudu (VIO) tarewa, kwacewa ko kuma cin tarar masu ababen hawa, hukumar ba ta da hurumi kan hakan."

Wannan hukuncin dai ya shafi har manyan jami'an hukumar VIO da suka hada da daraktan zirga zirgar tituna, kwamandan yankin Jabi da sauransu.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Jaridar The Punch ta rahoto cewa har da ministan babban birnin tarayya Abuja a cikin wadanda ake karar.

An lakadawa jami'in VIO duka

A wani labarin, mun ruwaito cewa gungun yan achaba sun lakadawa wani jami’in hukumar VIO dukan tsiya a babban birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce 'yan acaban sun daki jami'in VIO din ne a lokacin da ya yi kokarin kama babur din daya daga cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.