An cinna wa motocin FRSC da VIO wuta a Legas

An cinna wa motocin FRSC da VIO wuta a Legas

- Fusatattun matasa da ake kyauta zaton 'yan daba ne sun kone ofishin hukumar FRSC da VIO

- Matasa sun cinna wa motocci kimanin 30 wuta ciki har da motoccin da jami'an hukumar suka kama daga masu tuki

- Kazalika, wasu matasan sun tafi sun kone manyan motoccin daukan fasinjoji na BRT da ake ajiye a Berger a Legas

An cinna wa motocin FRSC da VIO wuta a Legas
An cinna wa motocin FRSC da VIO wuta a Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSARS: An kashe mutum 3, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja

An cinna wuta a ofisoshin hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC da jami'an kula da ingancin motocci, VIO, da ke unguwar Ojudu a jihar Legas.

The Punch ta ruwaito cewa wasu ganau sun ce sun ga motocci da dama da aka kona.

Majiyar Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa har zuwa karfe 2.20 na rana ba a kammala kashe wutan ba.

Kazalika, 'yan daba sun kuma cinna wuta a tashar da aka ajiye manyan motoccin daukan fasinja na BRT da ke Berger a jihar Legas.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas

Daya daga cikin wadanda abin ya faru a idonsu mai suna Ola ya ce, "An kona fiye da motocci 30. Abin ya shafi motocci da dama da hukumar ta kwace. Ginin ofishin yana ci da wuta."

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, Ƴar gidan gwamnan Kano, Fatima Ganduje-Ajimobi ta magantu a kan zanga-zangar #ENDSARS da ake don nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram ranar Asabar, 17 ga Oktoba, tayi kira ga mutane su mallaki katin zaben su sannan kuma bayan ya kaɗa kuri'arsa ya tabbatar an kirga kuri'ar tasa.

Anasa bangaren, mijinta Idris Ajimobi ya yi kira ga matasa da su tabbatar sun tanadi katin zabensu don tunkarar babban zaben 2023.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164