Reshe ya juye da mujiya: Gungun yan Achaba sun lakada ma jami’an VIO dan banzan duka

Reshe ya juye da mujiya: Gungun yan Achaba sun lakada ma jami’an VIO dan banzan duka

Wasu gungun yan Achaba sun lakada ma jami’in hukumar kula da ababen hawa, VIO, dukan tsiya a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Kaakakin hukumar, Kalu Emetu ya bayyana ma NAN haka a ranar Talata 24 ga watan Afrilu, inda yace yan Achabar sun daka wani jami’insu mai suna Abubakar Eyge, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Dubun yan bindigar da suka kashe Dansandan dake gadin gonar Magu ta cika

Emetu ya bayyana cewar lamarin ya faru ne a daidai shataletalen Area 1 na unguwar Garki dake babban birnin tarayya Abuja, inda yace yan Achaban sun doki jami’in ne a daidai lokacin da jami’in VIO yayi kokarin kama babur din dan Achabar.

Kaakakin yace wannan na daya daga cikin hatsarin aikin VIO, “Da ba dan jama’an gari sun taimaka ba, da sun nakasa shi, amma a yanzu jami’in namu na samun kulawa a wani Asibiti, amma a yanzu haka mun kai maganan ga hannun Yansanda.”

Haka zalika, Kaakaki Emetu ya bayyana cewa hare haren da ake kai ma jami’an VIO ya yawaita a garin Abuja, zuwa yanzu an kashe jami’ansu guda bakwai a ire iren hare haren nan tun shekarar 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel