Kano: Hisbah Ta Yi Sababbin Dokoki, Ta Hana Mata Hawa Keke Napep daga Karfe 10
- Hukumar Hisbah ta haramtawa maza da mata yin hira a cikin mota mai bakin gilashi da zarar karfe 10:00 na dare ta yi a Kano
- Hisbah ta kuma haramta duk wani nau'in cacar wasanni a jihar tare da cewa za ta cafke masu ba da hayar gidaje ana aikin ashha
- Hukumar ta kuma haramtawa mata hawa Keke Napep daga karfe 10:00 wanda Abba Hassan Gezawa ya ce akwai bukatar Hisbah ta sassauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A yayin da ta fitar da sababbi da kuma nanata tsofaffin dokoki, hukumar Hisbah ta Kano ta haramta duk wani nau'in cacar wasanni a jihar
Mataimakin kwamandan hukumar, Dakta Mujaheed Aminuddeen ne ya bayyana hakan yana mai jaddada sabon yunkurin da Hisbah ke yi na yaki da badala.
A wani rahoto na jaridar Daily Trust, Dakta Mujaheed ya ce Hisbah ta sake dawo da atisayen 'yaki da badala' domin damke mutane ko kungiya da ke yada badala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hisbah: 'An hana caca da hira a mota'
Ya ce hukumar za ta zage damtse domin tabbatar da tsafta a dabi'un al'umma yana mai cewa Hisbah za ta fara cafke masu ba da hayar gidaje ko shaguna.
A cewar Dakta Mujaheed, duk wanda aka kama ya ba da hayar gida domin a yi amfani da shi matsayin gidan mata masu zaman kansu zai fuskanci fushin hukumar.
Hisbah ta ce babu hira a mota mai bakin gilashi
Hukumar Hisbah ta kuma sake waiwayar samari da 'yan mata a cikin sababbin dokokinta, inda ta haramtawa masoya yin hira a mota mai duhun gilashi.
Mataimakin kwamandan hukumar ya ce babu wanda zai hana maza da mata yin hira, amma da zarar dare ya yi, to an haramta hira a mota mai duhu.
Kano: An hana mata hawa Napep
Game da barace-barace a kan titunan Kano kuwa, hukumar Hisbah ta ce za ta fara cafke matan da ke yin bara har dare ya yi.
Dakta Mujaheed ya kuma ce Hisbah ta damu kan yadda 'yan mata ke shiga harkar lalata a jihar, don haka ne suka dauki mataki a kai.
Ya ce daga yanzu an haramtawa kowacce mace hawa Keke Napep bayan karfe 10:00 na dare inda ya ce za a cafke duk wadda aka kama.
Mataimakin kwamandan ya kuma gargadi wadanda za su iya yunkurin karya dokokin yana mai cewa akwai hukunci mai tsanani da ke jiransu.
Me mutanen Kano ke cewa?
A zantawar Legit Hausa da wasu mazauna jihar Kano, sun jinjinawa hukumar Hisbah kan dawo da yaki da rashin da'a, sai dai sun ce dokar hana hawa Keke-Napep ta yi tsauri.
Abba Hassan Gezawa ya ce akwai lokuta da dama da mata kan yi dare idan suka je wani gari suka dawo, ko kuma lalura ta zuwa asibiti ta kama su, wanda ya kamata a duba.
Abba Gezawa ya kuma ce matsalar cacar wasanni ta zama ruwan dare yanzu inda matasa ke iya yin cacar a cikin wayoyinsu ba tare da sunje shagon buga caca ba.
Ya ba hukumar Hisbah shawara kan cewa ta rika shirya taro na gama gari domin wayar da kan matasa kan illolin yin caca a waya, wanda shi ne zai fi fa'ida sosai.
Hisbah ta yi doka kan bukukuwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramtawa maza ma su lura da saka sauti da aka fi sani da DJ aiki a bukukuwan mata.
Babban kwamandan Hisba na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wanda ya bayyana hakan ya ce hakan zai tsaftace jihar daga cakuduwar maza da mata ba bisa ka'ida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng