Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'addan Boko Haram

Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'addan Boko Haram

  • Dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasara kan miyagun ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Sojojin sun samu nasarar kuɓutar da mutane 40 da ƴan ta'addan suka yi garkuwa da su a jihar da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Kakakin rundunar MNJTF ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar ceto mutane 40 da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a Borno.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun kai farmaki sansanin 'yan ta'adda, sun sheke miyagu masu yawa

Sojoji sun yi nasara kan 'yan Boko Haram
Sojoji sun ceto mutane 40 a hannun 'yan Boko Haram Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin rundunar MNJTF, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce sojojin suna aiki ne a ƙarƙashin sashe na uku a Monguno, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da ƴan ta'addan suka yi garkuwa da su sun haɗa da maza takwas, mata takwas, da kuma ƙananan yara 24, rahoton jaridar Sahara Reporters ya tabbatar.

Boko Haram: Yadda sojoji suka ceto mutane

"Sojojin a yayin wani farmakin da suka kai a yankin ƙananan hukumomin Kukawa da Baga, sun tare wasu gungun ƴan ta'addan Boko Haram da ke jigilar mutanen da suka yi garkuwa da su."
"Ƴan ta'addan sun gudu bayan sun ci karo da sojojin, inda suka bar mutanen da suka sace, waɗanda aka ceto su nan take. Mutanen da aka ceto sun haɗa da maza takwas, mata takwas da ƙananan yara 24."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram

"Binciken farko ya nuna cewa ana jigilar mutanen da aka yi garkuwa da su ne daga wani sansanin Boko Haram a Dogon Chikwu."

- Laftanal Kanal Olaniyi Osoba

Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa jirgin yaƙin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ya kai farmaki kan sansanin ƴan ta'adda a jihar Kaduna.

Jirgin yaƙin na rundunar Operation Whirl Punch (OPWP) ya lalata sansanin ƴan ta'adda da ke dajin Yadi a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng