Yadda Aka Kashe Rikakken Dan Bindiga, Kachalla Mai Shayi a Harin Kwantan Bauna

Yadda Aka Kashe Rikakken Dan Bindiga, Kachalla Mai Shayi a Harin Kwantan Bauna

  • Fadan ramuwar gayya ta kara kamari a tsakanin dabar 'yan bindiga ta Kachalla Yellow Mai Bille da ta marigayi Kachalla Nagala
  • An rahoto cewa yaran Kachalla Nagala sun yi wa na hannun daman Kachalla Mai Bille kwanton bauna tare da kashe shi
  • An halaka fitinannen dan bindiga Kachalla Mai Shayi da wasu yaransa 12 ne a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamafara - Rahotanni sun bayyana cewa an halaka gawurtaccen dan bindiga Kachalla Mai Shayi, wanda ya addabi yankin Zamfara.

An ce dabar marigayi Kachalla Nagala ne suka kaddamar da harin kwantan bauna kan Kachalla Mai Shayi a tsakanin kauyen Buroyi da Buzaye.

Kara karanta wannan

Rikici ya rincabe tsakanin dabar yan ta'adda 2, rayuka sun salwanta

An kashe rikakken dan bindiga Kachalla Mai Shayi a rigimar daba a Zamfara
Yaran Kachal;a Nagala sun halaka dan bindiga, Kachalla Mai Shayi a harin kwanton bauna.
Asali: Original

An halaka Kachalla Mai Shayi

Rahoton da Zagazola Makama ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya nuna cewa an yi artabun ne a gundumar Bini, karamar hukumar Maru, jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin wannan harin kwantan baunar, an ce Kachalla Mai Shayi da dakarunsa 12 ne suka bakunci lahira.

Rahoto ya nuna cewa Kachalla Mai Shayi ya kasance wani babban jigo a dabar shugaban 'yan ta'adda Kachalla Yellow Mai Bille.

Fadan ramuwar gayya ya barke

Ana ganin cewa wannan harin na daga cikin hare-haren ramuwar gayya tsakanin bangarori daban daban na 'yan ta'addan da suka addabi Zamfara.

Rahoton ya ce an fara 'ba a ga maciji' tsakanin dabobin bayan Kachalla Yellow Mai Bille ya kashe Kachalla Nagala, lamarin ya tayar da kura.

Mabiyan marigayi Kachalla Nagala yanzu haka suna kan farautar Yellow Mai Bille, Sojan Zakwaui da kuma Yellon Emir domin daukar fansar mai gidansu.

Kara karanta wannan

Hassan Nasrallah: Dalilin da ya sa kasar Isra'ila ta kashe shugaban sojojin Hezbollah

An rahoto cewa wannan takun sakar da ake yi tsakanin dabobin biyu ya jawo asarar rayukan 'yan bindiga da dama musamman jagororinsu.

An halaka Kachalla Makore

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka wani hatsabibin dan bindiga da ya addabi Zamfara, Kachalla Makore.

Rahotanni sun ce an sheke Makore ne a hanyarsa ta zuwa ɗauko gawar Sani Black, da yan banga suka kashe a yankin Ɗan Sadau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.