Nasrun Minallah: Dakaru sun sheke 'yan bindiga 53, kwamandojinsu 5 a jihar Zamfara

Nasrun Minallah: Dakaru sun sheke 'yan bindiga 53, kwamandojinsu 5 a jihar Zamfara

- Dakarun sojin kasan Najeriya karkashin atisayen Operation Tsare Mutane sun sheke 'yan bindiga 48 da kwamandojinsu 5

- Hakan ta faru ne a samamen da suka kai sansanonin 'yan bindigan dake jihar Zamfara da jihohi masu makwabtaka da su

- Kwamandojin da aka halaka sun hada da Yellow Mai-Bille, Sani Meli, Dan- Katsina da Sama'ila Bakajin Bari

A daren Lahadi ne rundunar sojin Najeriya tace dakarun runduna ta 8 da aka tura yakar 'yan bindiga da suka addabi Zamfara da jihohi dake da makwabtaka dasu sun kashe kwamandojin 'yan bindiga 5 tare da wasu miyagu 48 bayan musayar wuta da aka yi.

Har ila yau, dakarun sun yi kokarin ceto mutum 18 da aka yi garkuwa dasu daga sansanin 'yan bindigan, Vanguard ta ruwaito.

Birgediya janar Mohammed Yerima, daraktan hulda da jama'a na sojin kasa, wanda ya sanar da hakan a wata takarda ya kara da cewa an tarwatsa sansanin 'yan bindiga masu yawa inda aka samo miyagun makamai.

KU KARANTA: Wasu 'yan Najeriyan basu tausayin kasarsu ko kadan, Shugaba Buhari

Nasrun Minallah: Dakaru sun sheke 'yan bindiga 53, kwamandojinsu 5 a jihar Zamfara
Nasrun Minallah: Dakaru sun sheke 'yan bindiga 53, kwamandojinsu 5 a jihar Zamfara. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan ta'addan ISWAP sun tarwatsa sansanin soji a jihar Borno

Ya ce, "Dakarun runduna ta 8 ta sojin kasa dake aiki a Zamfara da sauran jihohi sun samu manyan nasarori a yaki da 'yan bindiga da suke yi.

"Rundunar tun farko ta kaddamar da sabon atisaye mai suna Operation Tsare Mutane bayan umarnin da suka samu daga shugaban sojin kasa, Laftanal Kanal Ibrahim Attahiru.

"Babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Usman Yusuf ya kaddamar da atisayen wanda zai fara daga 23 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afirilun 2021 a karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara.

"Cike da nasara dakarun suka tarwatsa sansanonin 'yan bindigan dake Jaya, Kadaya da Bayan ruwa da sauransu.

"Dakarun sun yi nasarar sheke 'yan bindiga 48 yayin da shugaban 'yan bindigan yankin, Jummo ya samu miyagun raunika a kafafunsa. Dakarun sun ceci mutum 18 da 'yan bindigan suke rike dasu.

"An samo bindigogi kirar AK47 8 da wasu miyagun bindigogi hudu daga 'yan bindgan.

“Kwamandojin 'yan bindigan 5 da suka hada da Yellow Mai-Bille, Sani Meli, Dan- Katsina da Sama'ila Bakajin Bari duk sun sheka lahira yayin da Nasanda ya sha da kyar."

A wani labari na daban, 'yan bindiga da ake zargin mambobin IPOB ne sun kai mugun farmaki ofishin 'yan sanda dake Odoro Ikpe a karamar hukumar Ini ta jihar Akwa Ibom.

Jami'ai shida sun rasa rayukansu a harin da aka kai a sa'o'in farko na ranar Asabar, 8 ga watan Mayu, The Punch ta ruwaito haka.

Hakazalika, a yayin bada rahoton harin, The Cable ta ce wannan ne karo na biyu da ake kai hari cikin mako daya a jihar ta kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel