Hotuna: Dakarun Soji Sun Kai Harin Kwantan Bauna, Sun Halaka 'Yan Boko Haram 7 a Borno

Hotuna: Dakarun Soji Sun Kai Harin Kwantan Bauna, Sun Halaka 'Yan Boko Haram 7 a Borno

  • Zakakuran dakarun sojin Najeriya sun yi ruwan wuta kan mayakan Boko Haram a wani harin kwanton Bauna da suka kai musu a Bama
  • Bayanan sirri sun isa kunnen sojin kan cewa 'yan ta'addan na dawowa daga kasuwa, lamarin da yasa suka tare su tare da halaka 7 a cikinsu
  • Daya tak da ya tsere ya sanar da kwamanda Abu Hassana cewa an kashe masa dakarunsa, tuni suka tarkato tare da kai hari kan sojoji amma basu samu nasara ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai, OPHK, sun kai harin kwantan bauna kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Zakakuran sojin Najeriyan sun kai harin ne a yankin Kasuwan Daula dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Dakarun Soji
Hotuna: Dakarun Soji Sun Kai Harin Kwantan Bauna, Sun Halaka 'Yan Boko Haram 7 a Borno. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wani jami'in sirri ya sanar da Zagazola Malama, kwararre wurin yaki da ta'addanci kuma mai kiyasi a fannin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa dakarun sun samu wannan nasarar ne bayan sun samu bayanan sirri kan cewa 'yan ta'addan suna dawowa daga kasuwa bayan sun yi wasu harkokin kasuwanci.

Dakarun sojin da suka fita sintiri sun samu bayanai kan al'amuran 'yan ta'addan kuma suka yi kwanton bauna tare da jiransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin musayar luguden wuta, dakarun sun saki ruwan wuta kan 'yan ta'addan inda suka halaka bakwai a take yayin da daya tak ya tsere.

Zagazola ya gano cewa, 'dan ta'addan da ya tsere ya isa sansanin Abu Hassana, babban kwamandan kungiyar ta'addanci kuma ya sanar masa cewa an kashe masa mutanensa.

Da gaggawa Abu Hassana ya tarkato mayakansa kuma suka shiga garin Bama inda suka yi yunkurin kai hari kan dakaraun birged ta 21.

Daga isarsu wurin karfe 6:40 na yamma, 'yan ta'addan Boko Haram din sun fara harbe-harbe, lamarin da ya gigita jama'a mazauna garin.

Dakarun da ke zaune cikin shiri, sun yi musu ruwan wuta, lamarin da yasa 'yan ta'addan suka tsere babu shiri.

Soji Sun Ceto 'Yan Matan Chibok 3, Sun Damke Bukar Abatcha, mai Kaiwa 'Yan Ta'adda Makamai

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro a ranar Alhamis ta bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai sun cafke mai kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a yankin Asokoro dake babban birnin tarayya na Abuja.

Hakazalika, sun damke wani 'dan kasar ketare dake samarwa 'yan ta'adda makamai kuma dillalin makamai mai suna Abatcha Bukar tare da wasu 'yan ta'adda 13 a jihar Borno.

Punch ta rahoto cewa, daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan a zantawar da yayi da manema labarai a Abuja.

Yace an samu nasarar ceto 'yan matan Chibok uku da wasu mutum 19 da aka yi garkuwa da su a cikin lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel