Mummunan Hatsari Ya Yi Ajalin Mace Mai Shayarwa da wasu Mutane 3 a Zamfara
- Wani mummunan al'amari ya faru a randan otal din Gusau da ke jihar Zamfara inda wata tirela ta murkushe mutane hudu har lahira
- An rahoto cewa direban motar na tuki ne ta baya baya, inda ya bi ta kan wasu babura da ke dauke da mutanen gudu hudu
- Shedun gani da ido sun bayyana cewa direban tirelar ya ranta a na kare domin tsira da rayuwarsa ganin aika aikatar da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Rahotanni sun bayyana cewa wata tirela ta murkushe mutane hudu ciki har da mace mai shayarwa a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
An ce tirelar ta yi baya baya ta bi ta kan wasu babura da ke dauke da mutanen hudu, inda nan take suka ce 'ga garinku nan.'
Gusau: Tirela ta kashe mutane 4
A cewar rahoton AIT News, wani ganau ya ce direban tirelar na tuka motar ta baya baya ne a lokacin da ya murkushe wadanda abin ya rutsa da su suka mutu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mummunan lamari ya afku ne a randan otal din Gusau da misalin karfe 8:30 na safiyar Lahadin nan.
Ganin aika aikar da ya yi, an ce direban ya gudu domin tsira da ransa a tunanin zai iya gamuwa da nasa ajalin a hannun fusatattun mutane.
FRSC ta dauke gawar mutanen
Mutanen da suka ziyarci wurin da lamarin ya faru sun tarar da gawarwakin mutanen hudu da suka hada da mai shayarwa kwance cikin jini.
Daga bisani ne aka ce jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), sun kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa tare da kai su asibiti.
Mutane 6 sun mutu a hatsari
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani mummuna hatsari ya rutsa da mutum 23 a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, inda mutum shida suka mutu, 11 suka jikkata.
An ce hadarin motan ya afku ne a tashar Aliko da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata, 2 ga watan Janairun 2024 da misalin karfe 06:25 na safe.
Asali: Legit.ng