Zaki Ya Hallaka Dan Bauchi a Gidan Zoo da Ke Dakin Karatu na Tsohon Shugaban Kasa
- Wani matashi dan jihar Bauchi ya gamu da ajalinsa bayan zaki ya hallaka shi a jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya
- Matashin, Babaji Daule ya rasa ransa sanadin farmakin zaki a gidan zoo da ke dakin karatu na Olusegun Obasanjo
- An ce matashin ne ke kula da zakin inda ya manta bai kulle wurin da aka kulle shi ba wanda ya yi sanadin kufcewarsa tare da kai masa hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - An shiga alhini bayan wani zaki ya yi ajalin matashi a gidan zoo da ke birnin Abeokuta a jihar Ogun.
Marigayin mai suna Babaji Daule dan asalin jihar Bauchi ya gamu da tsautsayin a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.
Yan bindiga sun tabbatar da kisan matashin
Kakakin rundunar yan sanda a jihar, Omolola Odutola ita ta tabbatar da haka a yau Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Odutola ta ce lamarin ya faru ne a gidan zoo da ke dakin karatu na tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Rahotanni sun tabbatar da cewa matashin ya manta bai kulle inda zakin ya ke ba lokacin da ya zo ba shi abinci.
Yadda zakin ya hallaka matashi a Ogun
Hakan ya yi sanadin kufcewar zakin tare da kai farmaki kan matashin da ke kula da shi wanda ya yi sanadin mutuwarsa.
Daga bisani an dauki gawar matashin zuwa asibitin kwararru na Ijaye domin adana ta, kamar yadda TheCable ta ruwaito.
Har ila yau, an tabbatar da cewa an bindige zakin da ya kufce daga wurin adana shi domin tseratar da sauran al'umma.
Dorinar ruwa ta hallaka dattijo a Kebbi
Kun ji cewa wani dattijo mai shekaru 60 ya gamu da ajalinsa a jihar Kebbi bayan dorinar ruwa ta kai masa farmaki a ranar Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024.
Marigayin mai suna Mallam Usman Maigadi ya kasance dogarin sarkin Yauri, Muhammad Zayyanu-Abdullahi na tsawon lokaci.
Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin da kuma masarautar Yauri da ke jihar kan wanna abin takaici.
Asali: Legit.ng