'Yan sanda sunyi karin haske kan batar kudi a gidan Zoo na Kano

'Yan sanda sunyi karin haske kan batar kudi a gidan Zoo na Kano

Rundunar 'Yan sanda na Jihar Kano ta yi tsokaci kan labarin da ke yaduwa na cewa goggon biri ya hadiye zunzurutun kudi naira miliyan 6.8 da aka ce ciniki ne na kwanaki 5 da a kayi a Zoo ne yayin bikin Sallah.

Mai magana da yawun 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna ya yi karin bayani kan batun a hirar da ya yi da Daily Nigerian.

A cewarsa, an yi wa 'yan sanda waya cewa wasu bata gari sun kai hari gidan Zoo din cikin dare kuma suka sace naira miliyan 6.8.

Ya kara da cewa bayan samun korafin, rundunar ta aika da jami'an ta cikin gaggawa zuwa inda abin ya faru.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

Haruna ya kara da cewa an kama mutane 10 ciki har da ma'aikata da masu gadi da ke aiki a gidan Zoo din.

"Eh, an kira mu an fada mana cewa cinikin kwanaki biyar da aka samu yayin bikin Sallah a Zoo din Kano ya yi batan dabo.

"Mun aika jami'an mu cikin gaggawa. A yanzu, mun kama mutane 10 ciki har da masu gadin da ma'aikatan fannin kudi na Zoo din," inji shi.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin don gano gaskiyan abinda ya faru.

A bangarensa, shugaban gidan Zoo din, Umar Kabo ya tabbatar da batan kudaden kuma ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

Kabo ya shaidawa BBc cewa "Ba zan ce komai kan lamarin ba domin ana gudanar da binike. 'Yan jarida da dama sun zo wuri na amma ba na son inyi magana a kan batun. Abinda zan iya cewa kawai shine kudin ya yi batan dabo".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel