An gano barnar da Zaki ya tafka a gidan 'Zoo' na Kano kafin a kama shi

An gano barnar da Zaki ya tafka a gidan 'Zoo' na Kano kafin a kama shi

Da yammacin ranar Asbar ne wani Zaki ya kwace a gidan adana namun jeji (Zoological Garden) kuma ba a samu nasarar kama shi ba sai da safiyar ranar Lahadi.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa zakin ya yi kutse zuwa kejin adana Jimina, inda ya cinye guda daga cikinsu a daren ranar Asabar.

Daga bisani masu kula da dabbobin da ke gidan 'Zoo' din sun yaudari Zakin da wasu Akuyoyi biyu domin ya fito daga kejin adana Jiminonin gidan.

Sa'idu Gwarzo, shugaba a gidan Zoo na Kano ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa an samu Zakin ne a cikin farfajiyar kejin adana Akuyoyi bayan ya cinyesu gaba daya.

"Mun rufe shi a cikin kejin Akuyoyi domin mu yi amfani da hikima wajen saka shi barci kafin mu mayar da shi cikin farfajiyar kejin da muke ajiye shi," a cewarsa.

DUBA WANNAN: APC ta nada gwamnoni biyu daga arewa su jagoranci yakin neman zabe a Kogi da Bayelsa

Da safiyar ranar Lahadi ne, Legit.ng ta wallafa labarin cewa babban manajan darektan gidan adana namun daji na (Zoological Garden) Kano, Alhaji Usman Gwadabe, ya tabbatar da cewa kwararru sun samu nasarar kama Zakin da ya fice daga wurin ajiyarsa da yammacin ranar Asabar.

Gwadabe ya ce kwararrun sun yi amfani da hikimar kimiyya ta sa dabbobi masu hatsari bacci kafiin su samu nasarar kama Zakin da safiyar ranar Lahadi.

Shugaban ya shaida wa manema labarai a garin Kano cewa kwararrun sun samu nasarar kama Zakin tare da hadin gwuiwar jami'an 'yan sanda da sauran jami'an tsaro.

Ya kara da cewa kwararrun da jami'an tsaron na kokarin ganin sun mayar da Zakin zuwa cikin kejnsa da ke gidan 'Zoo' din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel