Yemi Cardaso Ya yi Rugu Rugu da Darajar Naira cikin Watanni 12 a Bankin CBN

Yemi Cardaso Ya yi Rugu Rugu da Darajar Naira cikin Watanni 12 a Bankin CBN

  • Makasudin nada Yemi Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya shi ne ya taimaka a farfado da tattalin arziki
  • Shekara guda da ‘yan kai kenan da canza gwamnan CBN amma sai dai Naira ta kara rasa kima maimakon ta dada daraja
  • Dalar Amurka ta na cigaba da sukuwa a kan kudin Najeriyan kuma har gobe ana fama da matsalar hauhawar farashin kaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Naira ta rasa fiye da rabin kimar da ta ke da ita a cikin shekara guda ta wuce bayan Yemi Cardoso ya karbi rikon babban banki.

A maimakon a ga Naira ta kara daraja a kasuwa, sai akasin haka ake gani a karkashin jagorancin Yemi Cardoso a bankin CBN.

Kara karanta wannan

'Zai kara aure?': Al'umma sun bayyana ra'ayoyi kan sakin Seaman Abbas

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN, Yemi Cardoso ya shekara a ofis Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tsare-tsaren Yemi Cardoso a CBN

Wani rahoto a Nairametrics ya ce alkaluma sun tabbatar da kudin Najeriyan ya karye da 51.49% daga Satumban bara zuwa yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 22 ga watan Satumban 2023, an saida Dalar Amurka a kan N747.76 a Najeriya, a yanzu kuwa Dalar ta haura N1, 541.

Asusun waje ya karu amma Naira ta fadi

An samu wannan karaya ne a sakamakon daidaita farashin kudin kasashen ketare da CBN ya yi bayan Bola Tinubu ya hau mulki.

Duk da ana ikirarin asusun kudin kasar wajen Najeriya ya karu, darajar Dalar ba ta karye ba bayan an yi waje da Godwin Emefiele.

Daga jaridar Tribune aka fahimci a shekara gudan, asusun kudin wajen Najeriya ya karu da 12%, aka samu cigaba a gwamnatin nan.

A Satumban 2024 aka ji cewa akwai $37.39bn a asusun waje wanda shi ne mafi yawan abin da aka tara a mulkin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Litar fetur ta koma N2500 bayan an fusata 'yan kasuwa, gwamnati ta dauki mataki

A kokarinsa na inganta tattalin arziki, Yemi Cardoso ya fito da dabarun da yake tunani za su magance hauhawar farashin kaya.

Ganin yadda har yanzu ake fama da tsadar kaya a kasuwa ya sa wasu masana suke ganin Cardoso bai tabuka abin kirki a bankin ba.

A gefe guda wasu suna ba shi uzurin an damka masa tattalin arziki ya na tangal-tangal, akwai masu ra’ayin cewa ya cancanci yabo.

Cardoso ya ci buri da matatar Dangote

Ana da labarin sabon gwamnan na CBN mai shekaru 57 a duniya ya dage wajen ganin ya farfado da kimar Naira da tattalin arziki.

Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana ƙwarin guiwar cewa matatar Ɗangote za ta taka rawa wajen rage wahalhalun da ake ciki a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng