CBN Ya Hango Sauƙin da Ƴan Najeriya Za Su Samu, Ya Yi Magana kan Matatar Ɗangote
- Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya ce man feturin Ɗangote zai daidaita farashin sufuri da rage tsadar abinci a Najeriya
- Cardoso ya bayyana haka ne a Abuja ranar talata, 24 ga watan Satumba, 2024 jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin MPC
- Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya karƙashin Bola Tinubu bisa matakin da ta ɗauka na cire harajin shigo da kayan abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ƴan Najeriya za su samu sauƙin tsadar sufuri da hauhawar farashin kayan abinci sakamakon fara aikin matatar Ɗangote.
Gwamnan babban banki watau CBN, Olayemi Cardoso ya ce man feturin Ɗangote zai taka rawa wajen rage tsadar sufuri da kayan abinci wanda ake ta kuka da su.
Cardoso ya bayyana hakan ne da yake zantawa da manema labarai yau Talata bayan kammala taron kwamitin MPC karo na 297 a Abuja, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankin CBN ya ce sauki na tafe
Ya ce kwamitin, wanda ke kula da harkokin kudi, ya gamsu cewa shigar man feturin Ɗangote kasuwa zai daidaita farashin sufuri.
"Kwamitin MPC na da ƙwarin guiwar man feturin matatar Ɗangote zai daidaita farashin sufuri, kuma zai taimaka matuƙa wajen rage farashin kayan abinci.
"Muna kuma sa ran zai taimaka wajen rage yawan bukatar canjin kuɗin kasashen ƙetare domin shigo da tataccen man fetur da kuma haɓaka asusun ajiyar waje."
- Olayemi Cardoso.
Wannan dai na zuwa ne bayan hukumar ƙididdiga ta kasa (NBS) ta tabbatar da samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Agusta.
CBN ya faɗi kalubalen da ake fuskanta
Gwamnan CBN ya ƙara da cewa ambaliyar ruwa, ƙarancin fetur da mafi muhimmanci matsalar tsaro a garuruwan manoma su ne kalubalen da abinci ke fuskanta.
"Bugu da kari, MPC ya yaba da kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na cike gibin ƙarancin abinci ta hanyar cire harajin shigo da su," in ji Cardoso.
CBN ya dawo da harajin yanar gizo
A wani labarin kun ji cewa babban bankin Najeriya CBN ya lashi takobin samun kusan Naira biliyan 50 nan da karshen shekarar nan ta 2024.
Babban bankin zai samu wadannan kudin shiga ne a dalilin harajin tsaron yanar gizo da aka sake dawo da shi a yanzu a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng