Fashin Banki a Arewa: Kotu Ta Yankewa Mutane 5 Hukuncin Kisa, Bayanai Sun Fito
- Mai shari’a Haleemah Salman ta babbar kotun jihar Kwara ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane biyar kan fashin bankin Offa
- Kotun ta kama wadanda ake zargin da laifuffukan da suka shafi fashi da makami, kashe 'yan sanda da farar hula da mallakar bindigogi
- Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan fashi sun farmaki bankin Offa a Afrilun 2018 inda suka kashe mutane 32
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - A ranar Alhamis ne wata babbar kotun jiha da ke Ilorin, jihar Kwara ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutane biyar da ake tuhuma da laifin fashin bankin Offa.
Legit Hausa ta tuno cewa wadanda ake zargin sun farmakin bankin Offa ne a ranar 5 ga watan Afrilun 2018 inda aka kashe mutane 32 ciki har da 'yan sanda tara.
An yanke hukuncin kisa ga 'yan fashi
Wadanda kotun ta yankewa hukuncin kisan su ne Ayoade Akinnibosun, Azeez Salahudeen, Niyi Ogundiran, Ibikunle Ogunleye da Adeola Abraham, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da ta ke yanke hukuncin, Mai shari'a Haleema Saliman ta bayyana cewa an samu wadanda ake zargin da aikata laifin kitsawa, fashi da makami, kisan kai da mallakar makamai.
Mai shari'a Haleema ta ce wadanda ake zargin sun kashe mutane ciki har da 'yan sanda da farar hula a harin da suka kai bankin, wanda hukuncin laifinsu kisa ne
Masu gabatar da kara sun magantu
Premium Times ta rahoto, jagoran masu shigar da kara, Rotimi Jacob (SAN) ya ce sun samu damar tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun aikata laifuffukan.
Mista Jacob ya ce sun kwashe shekaru shida domin ganin an yi wa wadanda harin ya shafa adalci, kuma wadanda ake zargi su ne suka yi fashin tare da kashe mutane.
Ya ce ya na da yakinin kotun a yanzu ta gamsu da dukkanin hujjojin da masu gabatar da karar suka gabatar wanda zai sa ta yankewa wadanda ake zargin hukuncin da ya dace.
Harin Offa: An damke mutane 7
A wani labarin, mun ruwaito cewa an fara zaman makoki a jihar Kwara bayan da wasu 'yan fashi suka kai hari bankin Offa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Jami'an tsaro sun sanar da cewa sun samu nasarar damke mutane bakwai daga cikin wadanda ake zargin sun kai hari bankin tare da yin karin bayani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng