Siyasar Kwara: 'Yan fashin Offa sun isa kotu, Saraki yayi gum da bakinsa, lauya kuma ya janye

Siyasar Kwara: 'Yan fashin Offa sun isa kotu, Saraki yayi gum da bakinsa, lauya kuma ya janye

- An gurfanar da 'yan fashin Offa a gaban kotu

- Mutane 31 ne suka mutu ciki harda mai ciki

- Ana cigaba da bincike don gano ragowar

Siyasar Kwara: 'Yan fashin Offa sun isa kotu, Saraki yayi gum da bakinsa, lauya kuma ya janye
Siyasar Kwara: 'Yan fashin Offa sun isa kotu, Saraki yayi gum da bakinsa, lauya kuma ya janye
Asali: Facebook

An gurfanar da wasu mutum biyar da suka kai farmaki a bankin Offa a ranar 15 ga watan Afrilu 2018.

A lokacin da suka kai harin mutane 31 ne suka rasa rayukan su ciki harda wata mai ciki da yan sanda biyu sannan sukayi gaba da makudan kudade.

Kafin jiya a gurfanar da wadanda ake zargin sun ambaci sunan Gwamna Abdulfatah Ahmed da Bukola Saraki. Lamari da ya ruruta siyasar jihar da ma ta kasa baki daya.

An kai mutane biyar da ake zargin su cikin fashi da kashe-kashen da akayi a Bankin Offa a ranar 15 ga watan Aprilu, 2018, na Offa Jihar gundumar Kwara kotun daukaka kara a gaban kotun Majistare na Ilorin

Hakanan kuma, mai bada shawara ga wanda ake tuhuma, Abulrasheed Lawal ya sanar da janyewar shi daga cigaba da wakiltan su a kotu.

Tuna da cewa a lokachin fashin, an kashe mutane talatin da suka hada da mata masu ciki da jami'an yan sanda guda biyu yayinda yan bindigan suka kwashe miliyoyin nairori

Tun kafin jiya, jama'ar da ake zargin fashi da makamin, Gwamna Abdulfatah Ahmad da Shugaban Majalisar Dajjitai Dakta Bukola Saraki sun nuna cewa ana zarginsu ne kawai. A yayin zaman, kotun ta bayyana cewa yan fashin da ake zargi da yin fashin na Offa suna da matsala don amsawa.

Tun kafin ranan, Kwamishinan yan sandan Jihar kwara, OC Kunle Iwalaiye, ya nuna cewa wannan lamarine da aka ambata da kuma la'akari da wasikar jihar kwara na Daraktan (DPP). Mista Iwalaiye ya kara da cewa, wadanda ake tuhumar sunada abubuwan da za su amsa acikin shawarwari na DPP AUST/ LED14 / V140 / 1457/738 da ranar 11 ga Nuwamba, 2018.

DUBA WANNAN: Yawan masu tabon hankali a kasar nan ya kai...

Dokar OC, wanda Mai Shari'a ASP Abdulkadir ya wakilta ya ce "a cikin wannan hali masu laifi da abubuwan da za su amsa. Muna neman wani kwanan wata don karin bayani game da cewa dole ne a yi musu hukunci a gaban kotun".

DPP ta umarci 'yan sanda su ci gaba da gudanar da bincike tare da ra'ayi kan kama wasu wadanda ake zargin da suka gudu. Duk da haka, mai bada shawara ga wanda ake tuhuma, Abulrasheed Lawal ya sanar da janyewar shi daga shari'ar bisa ga rashin bin doka

A yayin da ake gudanar da zaman kotun tace wadanda ake tuhumar akwai wasu laifuka akansu.

An bawa yan sandan damar zurfafa bincike don gano ragowar da suka gudu. An kuma maida kes din Abuja, karkashin ofishin IGP gaba daya, lamari da wasu ke gani an shirya ma bita-da kulli ne.

Mai girma alkalin kotun ya dage sausaran karan zuwa 6 ga watan Disemba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng