Gungun Yan fashi 15 sun kashe na kashewa, sun arce da makudan kudade daga wani Banki

Gungun Yan fashi 15 sun kashe na kashewa, sun arce da makudan kudade daga wani Banki

An samu rahoton wani tashin tashina a garin Offa dake jihar Kwara, inda wasu yan fashi da makami suka yi ma wani banki diran mikiya, suka kashe na kashewa, suka fasa bankin sa’annan suka arce da makudan kudade.

Legit.ng ta ruwaito akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a sakamakon harin, daga cikinsu akwai Yansanda guda biyu zuwa uku, a fashin da suka kwashe tsawon awanni suna shuka tsiyarsu, tun daga 4:45 zuwa 5:40

KU KARANTA: Shari’a sabanin hankali: An yanke ma barawon sigari da kwalaben giya hukuncin kisa

Bugu da kari Yan fashin sun yi ma bankin gagarumar shiri, inda suka dira da nakiyoyi, wadanda suka yi amfani dasu wajen fasa kofar bankin, sa’annan dauke da muggan bindigu masu sarrafa kansu, yayinda bayan fashin, suka yi awon gaba da motoci da dama.

Gungun Yan fashi 15 sun sun kashe na kashewa, sun arce da makudan kudade daga wani Banki
Bankin

Rahotanni sun tabbatar da cewar da far sai da suka fara isa ofishin Yansanda dake garin Offa, inda suka bindige dukkanin Yansandan da suka iske a can, a matsayin wata riga kafi da suka yi ma kansu, daga nan ne suka nufi bankin.

Bayan kammala ta’asar tasu ne, yan fashin sun kwace baburan jama’a, wadan suka yi amfani dasu wajen tserewa ta hanyar Igosun. Shi ma Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace yan fashin sun kai mutum 15.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng