Kisan gilla na jiya a Offa: 17 suka mutu, an fara makoki a yankin, hukuma ta damqe mutum bakwai

Kisan gilla na jiya a Offa: 17 suka mutu, an fara makoki a yankin, hukuma ta damqe mutum bakwai

- Maharan sun kai hari banki ne da saiyar juma'a

- Sun hallaka mutane da dama ciki harda 'yansanda

- Gaba daya garin ana makoki, an kuma baza jami'an tsaro

Kisan gilla na jiya a Offa: 17 suka mutu, an fara makoki a yankin, hukuma ta damqe mutum bakwai
Kisan gilla na jiya a Offa: 17 suka mutu, an fara makoki a yankin, hukuma ta damqe mutum bakwai

Kisan gilla da wadansu bata gari da ake tsammanin 'yan fashi ne, ya jawo asarar rayuka da yawa a garin Offa dake arewacin kasar nan a jiya a jihar Kwara.

An kai harin ne da safiyar juma'a a kan jama'a da jami'an tsaro, inda aka kashe mutane da suka zo banki domin cirar kudi da ma masu tsaro a wurin.

Sun kuma kwashi miliyoyin kudi a babbar motarsu sun yi awon gaba dasu.

Yanzu hukumomi sun saki adadin wadanda aka kashe cewa 17 ne, sannan sun ce sun kama akalla mutum bakwai da ake zargi suna da hannu cikin mummunan aikin.

DUBA WANNAN: Yan Indiya da basu yi wata bokon kirki ba

Su dai maharan, sun fara zuwa ofishin 'yan-sanda inda suka kashe 'yansanda bakwai, suka kuma kashe na kulle biyar, suka kwashi makamai suka nufi bankin. Can ne kuma suka kashe jama'a garin harbi a titi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng