Tinubu Ya Kunyata Majalisar Tarayya, Ya Ki Rattaba Hannu kan Kudurin da Aka Kawo

Tinubu Ya Kunyata Majalisar Tarayya, Ya Ki Rattaba Hannu kan Kudurin da Aka Kawo

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da kudirin dokar da ya nemi tsawaita wa’adin shekarun ritaya na ma’aikatan majalisar tarayya
  • Kudirin dokar ya nemi a kara shekarun ritayar ma'aikatan zuwa 65 (na haihuwa) ko kuma shekaru 40 (na gudanar da aikin gwamnati)
  • A wata wasika da ya rubutawa ‘yan majalisar, Tinubu ya ce ya ki amincewa da kudurin ne bayan dogon nazari da kuma tuntubar juna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ki amincewa da kudirin dokar kara wa jami’an majalisa da sauran ma’aikatan majalisar dokokin kasar wa’adin ritaya.

Kudirin dai ya nemi a tsawaita wa’adin ritayar ma’aikatan majalisar daga shekaru 60 zuwa 65 ko kuma daga shekaru 35 zuwa 40 na hidimar aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

Mutuwar Sanata ta dakatar da zaman majalisar tarayya, bayanai sun fito

Tinubu ya yi magana kan kudurin tsawaita wa'adin ritayar ma'aikatan majalisar tarayya
Tinubu ya ki amincewa da kudurin kara wa'adin shekarun ritayar ma'aikatan majalisar tarayya. Hoto: @NGRSenate, @officialABAT
Asali: Facebook

A wasikar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zaman majalisar, shugaba Tinubu ya ce ya yanke shawarar kin amincewa da kudirin, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dadewar kudurin a majalisar tarayya

An fara gabatar da kudurin ga majalisar tarayya ta bakwai amma ya gaza tsallakewa, sannan aka sake dawo da shi a majalisa ta takwas da ta tara, nan ma ba a dace ba.

An dawo da kudurin dokar a zauren majalisa ta 10 kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Aliyu Sani Madaki (NNPP, Kano) ne ya dauki nauyinsa.

Ya kai matakin karatu na biyu a majalisar a watan Oktoban da ya gabata kuma majalisar ta amince da shi a ranar 20 ga watan Disambar bara.

Duk da cewa majalisar dattawa ta yi watsi da kudurin da farko, amma ta lashe amanta tare da zartar da shi a ranar 31 ga Maris, 2024, inda ta mika wa shugaban kasa domin ya sa hannu.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su wataya: Tinubu ya sanya ranar fara biyan sabon albashin N70000

Tinubu ya ki amincewa da kudurin

The Punch ta ruwaito cewa a cikin wasikar da Sanata Godswill Akpabio ya karanta, shugaba Tinubu ya ce:

“Na rubuta wannan wasikar ne game da karin shekarun ritaya na jami’an majalisar dokokin tarayyar Najeriya da majalisar ta amince da shi kuma ta turo mani domin amincewa.
“Bayan na yi nazari sosai da kuma tuntubar juna a hankali, na yanke shawarar kin amincewa da kudirin. Na yi hakan bisa ga ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya ba ni."

Duk da kin amincewa da kudurin, Tinubu ya jinjinawa majalisar tarayyar kasar bisa amincewarsu kan kudurin tare da fatan za su kalli matakinsa ta fuska mai kyau.

An kara albashin 'yan majalisu

A wani labarin, mun ruwaito cewa an kara albashin sanatoci da na 'yan majalisar tarayya a Najeriya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce lakari da matsin tattali da ake fama da shi.

Ja’afar Ja’afar ya fito ya yi ikirarin cewa sanatan da ke daukar N13.5m a kowane wata yanzu ana biyansa N20m yayin da 'yan majalisar tarayya ke karbar N13.5m daga N8.5m.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.