Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar tarayya da wasu ma'aikata 150 sun yi murabus
Hukumar kula da ayyukan majalisar tarayya ta kasar nan, ta amince da ritayar magatakardanta, Mohammed Sani-Omolori tare da wasu ma'aikatanta 150.
Shugaban hukumar kula da ayyukan majalisar, Ahmed Amshi, ya bada wannan sanarwar a wata takardar da jaridar The Punch ta gani a ranar Laraba.
Tun a watan Fabrairun 2020 ya kamata Sani-Omolori ya yi murabus, amma gyaran da majalisar dattawan karo ta 8 ta yi wa sharuddan aiki ne yasa aka kai shi har tsawon shekaru biyar.
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, ta bayyana hakan da rashin bin ka'ida tare da take doka.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida
A wani labari na daban, Alakar da ke tsakanin ma'aikatar kwadago da majalisar dattawan kasar nan ta sake tabarbarewa a ranar Laraba a yayin da wasu wakilan majalisar da ministan kwadago, Chris Ngige suka samu rashin jituwa.
Rikicin ya fara ne bayan babban darakta a ma'aikatar kwadagon, Eyewumi Neburagho, wanda ya wakilci ministan aka gayyacesa don yin tsokaci a kan wata doka.
Kalamansa sun tada kura bayan da ya bukaci a dakatar da jin ta bakin jama'a tare da dokar har zuwa lokacin da kwamitin majalisar za su gayyaci ma'aikatar tare da tura mata dokar a rubuce.
Neburagho ya musanta cewa, a matsayinsa na daya daga cikin masu ruwa da tsaki, ba a tafiya da ma'aikatarsu a duk lokacin da aka zo jin ta bakin jama'a.
Sai dai su turo wakili a duk lokacin da suka samu rahoto daga manema labarai. Ya ce dole ne ma'aikatar ta san yadda dokar take da kuma yadda za ta shafi ma'aikatanta.
A don haka, ya yi kira ga kwamitin majalisar da su dakatar da duk wani aiki a kan dokar ko kuma su dakatar da duk wani abu da ya shafa dokar da zai hada da ma'aikatansu.
Matsayar ma'aikatar kwadagon sam bata yi wa kwamitin dadi ba don sun jaddada cewa sai sun ci gaba da ji ta kan bukatar.
Shugaban kwamitin, Sanata Uba Sani, ya ja kunnen ma'aikatar da ta guje bai wa majalisar dattawan umarnin yadda za su tafi da al'amuransu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng