NiMET: Za a Zabga Mamakon Ruwan Sama a Kano, Yobe da Wasu Jihohin Arewa 14

NiMET: Za a Zabga Mamakon Ruwan Sama a Kano, Yobe da Wasu Jihohin Arewa 14

  • A yayin da daminar bana ke shirin karewa, hukumar NiMET ta sanar da cewa za a tafka mamakon ruwa a jihohi 17 na Arewa
  • Binciken masana hasashen yanayi da ke a hukumar ta NiMET sun alamta cewa ruwan zai sauka a jihohin a lokuta daban daban
  • A hannu daya kuma, hukumar ta gargadi mazauna waɗannan jihohi da su yi taka tsantsan musamman yankunan gabar tekuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke hasashen yanayi a Najeriya, NiMET ta bayyana cewa wasu jihohin Najeriya za su fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Hukumar ta sanar da cewa akwai jihohin da ruwan ba zai yi karfi ba amma dai za a iya kwashe kwanaki uku ana tafka ruwan a jere.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a cin hancin N10000’

NiMET ta yi hasashen zuwa sama mai karfi a jihohin Arewa.
NiMET ta yi hasashen mamakon ruwa na kwanaki 3 a wasu jihohin Arewacin Najeriya. Hoto: Puneet Vikram Singh
Asali: Getty Images

Jihohin da ruwa zai yi karfi

Hasashen NiMET ya kuma nuna cewa za a yi kwarya kwaryan ruwan sama a kimanin jihohi 17 na Arewa, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar hukumar ta bayyana cewa za a tsula ruwan ne na kwanaki uku daga ranar Litinin, 23 ga watan Satumba har zuwa Laraba, 25 ga Satumbar 2024.

"Za a fuskanci ruwa mai karfi gami da tsawa a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihohin Neja, Nasarawa, Benuwai, Filato da Kwara.
"Da rana da kuma maraice za a sha ruwa marar karfi a wasu sassan Kwara, Abuja, Neja, Benuwai da Kogi."

- A cewar NiMET.

Lokutan da ruwa zai sauka a jihohi

The Punch ta rahoto hukumar ta kuma ce a saurari zuwan ruwan sama a safiyar ranar Litinin a jihohin Sokoto, Kebbi, da kuma Borno.

Kara karanta wannan

Bayan kama matashi da sata a Kano, masu kaya sun fadi sharadin yafe masa

Da yammacin ranar Litinin kuwa, NiMET ta yi hasashen ruwa zai sauka a jihohin Jigawa, Borno, Yobe, Taraba, Adamawa, Gombe, Bauchi, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sokoto.

Hukumar ta yi kira ga wadanda ke zauna a garuruwan da ambaliyar ruwa ke masu barazana da su dauki matakan kare rayukansu.

An kuma shawarci matafiya musamman na sufurin jiragen sama da su nemi bayanan yanayi daga shafin hukumar domin kare kansu daga barazanar ruwa da iska.

Jihohi 6 da za a zabga ruwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa NiMET ta gargadi wasu jihohin Arewa shida da su shirya ganin tsawa da iska mai karfi yayin da mamakon ruwa zai zuba a kwanaki masu zuwa.

Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta kasar ta ce jihohin Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna da Zamfara ne za su fuskanci mamakon ruwan saman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.